10/02/2026
Da Ɗumi Ɗumi
Gwamnan Kano Alhaji Abba K Yusuf Ya Cika Alkawarin Daukar Nauyin Zakaran Musabaqa Ta Duniya
Alhamdulillah, Gwamnan Jihar Kano ya cika alkawarin da ya dauka na daukar nauyin karatun wasu ‘yan asalin jihar Kano da s**a samu gagarumar nasara a gasar Musabaqar Al-Qur’ani ta duniya da aka gudanar a kasar Saudiyya.
Waɗanda s**a wakilci Nigeria su ne Malam Sunusi Bukhari da matarsa,
inda dukkansu s**a yi nasara a bangarorin da s**a fafata. Nasarar da s**a samu ta janyo farin ciki matuƙa, har ta sa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano ya dauki alkawarin daukar nauyin karatunsu domin ci gaba da inganta iliminsu.
Domin cika wannan alkawari, Gwamnan ya umarci Mai Girma Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano Ahmed Tijjani Sani Auwal da ya nemo musu jami’ar da za su ci gaba da karatu. Cikin yardar Allah, an same musu gurbin karatu a Jami’ar King Khalid University da ke kasar Saudiyya, wacce ita ce jami’a ta biyu mafi girma a kasar.
Malam Sunusi Bukhari da matarsa za su shafe tsawon shekara hudu a kasar Saudiyya suna karatu. Malam Sunusi zai yi karatu a bangaren Ilimin Addinin Musulunci da Tafsiri har zuwa matakin Digirin Dakta (PhD), in sha Allah. Ita kuma matarsa za ta karanci Computer Science.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkanin abubuwan da s**a shafi karatunsu, masauki, da bukatun da karatu ke bukata, gwamnatin jihar Kano ce za ta dauki nauyinsu gaba daya har su kammala karatunsu.
Al’ummar jihar Kano sun yabawa wannan mataki tare da yin addu’ar Allah ya saka wa Mai Girma Gwamnan Kano da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
Sai dai kuma, bayan wannan albishir, ana sa ran samun wani karin labari mai dadi daga kasar Saudiyya dangane da jihar Kano, wanda za a bayyana da safiyar gobe, in sha Allah.
Sunusi Muazu SSR Religious Affairs
Kano State Qur'anic Recitation Competition