06/05/2026
Ƙwayoyin Cuta Masu Yaɗuwa
Abubuwan da ke haddasa cututtuka masu yaɗuwa ga ɗan adam sun kasu zuwa manyan rukunoni guda biyar na halittu: Bacteria, Fungi, Protozoa, Helminths (tsutsotsi), da kuma Viruses.
Su Bacteria suna cikin rukunin "Bacteria domain", yayin da su kuma Fungi, Protozoa, da Helminths (tsutsotsi) ana sanya su ne a rukunin "Eukarya domain".
BAMBANCIN HALITTUNSU
Protists da Fungi: An bambance su da dabbobi da tsirrai saboda su halittu ne masu kwayar halitta (cell) guda ɗaya (Unicellular), ko kuma masu kwayoyin halitta da dama (wato multicellular) amma marasa complex structure.
Helminths (Tsutsotsi): Su kuma halittu ne masu sarƙaƙiya (complex) da kwayoyin halitta (cells) masu yawa (multicellular).
Yanayin Viruses.
Viruses sun bambanta kwarai da sauran halittun dana ambata. Su ba su da kwayar halitta (noncellular); wato ba su da (nucleus) ko sinadarin cytoplasm. Ba sa iya samar da energy na kansu, kuma ba su da ikon samar da sinadarin gina jiki (protein).
Saboda haka, sun dogara ne kacokan kan kwayoyin halittar da s**a shiga (host cells) domin su ninkaya ko su hayayyafa.
Wannan ya sa ake kiransu obligate intracellular pathogens (wato kwayoyin cuta da dole sai sun shiga cikin kwayar halittar wani sannan suke rayuwa).
To be continued...