14/01/2023
AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI.......
Wannan magana abar dubawa ce fa, yakamata ayi magana ta hankali, shin ba'a buga kudin bane, rinawa akayi?, in kuma an buga kuɗin mai yasa suke kodewa?, shin ba'ayi masu inganci bane?, duk da maƙudan kuɗaɗen da aka bawa babban Bankin kasa, don billahil azeem na jarraba nagani, in dai kasa ruwa a jikin auduga ka goge, kalar su tana fita, sannan mai yasa basu wadata ba a hannun jama'ar kasa, duk da wa'adin da aka dauka na wannan aiki?.
Lallai wannan magana ta honourable Gudaji Kazaure abu ne da yakamata ace an duba, kuma an wayar mana da kai, don muna da hakkin akan dukiyar kasar mu, muji ta ina aka kashe ta, mai akayi da ita, ba wai mu zura idanu wasu tsirarun mutane suna azurta kansu da iyalin su ba.
A kira gwamnan banki a gurfanar da shi gaban majalisa, ya bada bahasin ya akayi tunda dai kuɗin Nigeria bana gyatumarsa bane, kuɗin talakan kasa ne, ayi aka dauke shi ake biyansa, don haka indai ba wasu ne s**a ci kuɗin s**a dora shi akan abinda zai yi na, to Yakamata a gurfanar da shi, ya faɗi yaya aka haihu a ragaya.
Kudin kasa namu ne, domin mu akewa aiki dasu, tayaya za'a jefa mutane cikin fatara da talauci, ana kashe kuɗaɗe masu yawan gaske da sunan talaka amma kullum talakan kara shiga masifa yake?, babu wani abu da zaka taɓa kasamu sauki, tun daga kan harkar abinci tsaro da sauran abubuwan more rayuwa, lallai lokaci yayi daya kamata mu farka, mu bibiyi bahasin abinda yake wakana.
Don wallahi ko ansake zaben wasu maciya amanar dai za'a sake zaba indai ba'a yiwa tufkar hanci ba.
In sha Allah, idan wannan sakon yaje inda muke son yaje, muna jiran ba'asi domin Nima daga yau nabi sahun Gudaji Kazaure, in kumce shi dan siyasa ne, don kujerarsa yake magana, Ni kuma sai naga wani shegen dan siyasa a jiha ko a kasa da zaice naci naira biyar dinsa, ko ina da wata alaqa da shi ta siyasa da zan bashi kariya kan hakkin talaka.
Allah yasa muga alkairi, Allah ya ɗaga Nigeria!...