Dan Sarki

Dan Sarki Nigeria

Hon. Dasuki Ya Yi Gaisuwar Rasuwar Hajiya Hauwa'u Torankawa Dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar Kebbe/Tambuwal, Honarab...
23/05/2026

Hon. Dasuki Ya Yi Gaisuwar Rasuwar Hajiya Hauwa'u Torankawa

Dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar Kebbe/Tambuwal, Honarabul Abdussamad Dasuki (Santurakin Sakkwato) ya gabatar da gaisuwar rasuwar dattijuwa Hajiya Hauwa'u Torankawa a garin Yabo a yau Asabar.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shugabar mata ta jam'iyyar ADC a Kudancin Sakkwato, Hajiya Saratu Abubakar (VIO)

Honarabul Dasuki ya bayyana marigayiyar a matsayin dattijuwar kirki wadda ta rayu rayuwa tagari ta kuma komawa ubangiji a lokacin da aka fi bukatar ta tare da rokon ubangiji ya karbi bakuncin ta ya kuma albarkaci zuri'arta da dangogin ta Amin.

A gaisuwar da ya gabatar, matashin jajirtaccen dan majalisar yana tare ne da rakiyar Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Majalisa, Honarabul Attahiru Umar Danmadi da tsohon Kashiya a ma'aikatar kudi, Alhaji Arzika Bagidade.

TeamDasuki.
23/05/2026.

Hon Abdussamad Dasuki (Santurakin Sokoto) yayi gaisuwar rasuwar Dattijo Usman Sa’ad Tambuwal a Shiyyar Mabera da ke nan ...
23/05/2026

Hon Abdussamad Dasuki (Santurakin Sokoto) yayi gaisuwar rasuwar Dattijo Usman Sa’ad Tambuwal a Shiyyar Mabera da ke nan cikin birnin Sokoto. Allah ya masa rahama ya karbi bakuncin sa.

Santuraki na tare da rakiyar Sarkin Yamman Dogondaji, Alh. Nasiru Shehu, da tsohon Babban Darekta na Ma’aikatar Bunkasa Shigar Haraji ta jihar Sokoto, Alh. Murtala Dogondaji.

Good job boss
03/05/2026

Good job boss

02/05/2026
Hon. Abdussamad Dasuki, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kebbe/Tambuwal, ya gabatar da ƙuduri kan buƙatar fara aiki da...
30/04/2026

Hon. Abdussamad Dasuki, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kebbe/Tambuwal, ya gabatar da ƙuduri kan buƙatar fara aiki da kuma kammala ayyukan bunƙasa masana’antar motoci na ƙasa a Dogondaji da Bodinga, Jihar Sakkwato.

Cibiyar Hidimar Motoci ta Bodinga, wadda aka kammala a shekarar 2023 da kuɗin da ya haura naira biliyan 1, har yanzu ba a fara aiki da ita ba, yayin da Cibiyar Horar da Matasa ta Dogondaji aka yi watsi da ita.

Ya buƙaci a gaggauta kammala cibiyar horaswar tare da cikakken amfani da kayayyakin more rayuwa da ake da su domin samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa ƙwarewar matasa.

Address

Kofar Aiku Sokoto
Sokoto
840101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Sarki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share