09/11/2025
*_KA TUNA LAHIRARKA_ 005.*
*_“Ka Tanadi Abin Da Zaka Tafi Da Shi”_*
*Ya kai bawan Allah!*
Ka sani, babu mai tabbas da ranar da za ta zo ta ɗauke ka daga wannan duniya sai Allah.
Allah Madaukakin Sarki yace:
"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَلتَنظُرْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ لِغَدٍ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ"
*(“Ya ku waɗanda s**a yi imani! Ku ji tsoron Allah, kuma kowa ya duba abin da ya tanadar domin gobe (lahira), kuma ku ji tsoron Allah. Lallai Allah Masani ne game da abinda kuke aikatawa.”)*
*Ka duba, me ka tanadar ?*
Shin kana da sadaka daza ta haskaka kabarinka ?
Shin kana da taimako da za a kira “Wannan shine ya taimaka mini saboda Allah” ?
Shin kana da wata hanya da addinin Allah ya amfana da kai ?
*Manzon Allah (SAW) yace:*"Idan mutum ya mutu, dukkan ayyukansa sun yanke, sai dai guda uku: *Sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko yaro nagari da yake yi masa addu'a."*
— Sahih Muslim
*Ya kai dan Adam!*
Ka tuna cewa dukiyar da kake tarawa, rana ɗaya za ta zamo ba naka ba. Za a bar maka gida da kujeru, amma kai ka koma kabari. Abin da zai bika shine *ayyukan ka*.
*Imam Ibn Al-Jawzi (rahimahullah) ya ce:*
*"Mutane suna bauta wa duniya, su manta da lahira. Amma ranar da duniya ta kau, lahira zata bayyana – to me za su yi ?"*
*Don haka ka tanadi lahirarka kafin ka tafi.*
Ka bayar da sadaka, ka tallafa wa mabukata, ka taimakawa addinin Allah domin Allah yana cewa
*"مَن ذَا ٱلَّذِى يُقْرِضُ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًۭا فَيُضَـٰعِفَهُۥ لَهُۥ وَلَهُۥٓ أَجْرٌۭ كَرِيمٌۭ"*
*(“Wane ne zai bai wa Allah rance mai kyau (sadaka), Sai Allah ya ninka masa, kuma yana da lada mai girma.”)*
*Ya kai bawan Allah,* kayi qoqarin yin ayyukan alkhairi domin lahirarka
*Darul Khair Foundation*
Domin ayyukan saka solar a masallatai da kuma hada bohol da taimakon bayin Allah marasa lafiya da sauran ayyukan Alkhairi.
_Yaku bayin Allah kowa ya bada nasa taimakon domin a daukaka addinin