19/06/2025
Akwai wasu abubuwa guda uku da Isra'ila take son faruwar su a cikin wannan yakin, babba daga ciki shine tunda yanzu a duniya babu wata kasar da take da makamin da zai iya fasa wajen da Iran take kera makamai masu Linzami dake ƙarƙashin ƙasa sai America, babban burin Israel shine America tayi amfani da wannan makamin ta harbawa Iran. Tana ganin idan anyi haka toh Iran zata mika wuya nan take.
Akan hakan Trump ya tattauna da Prime Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a waya shekarn jiya, inda Trump yace masa America zata duba maganar. Jiya da yamma sai Trump ya zauna da shugabannin tsaron kasar, na fili dana boye akan matakin da za'a dauka akan Iran tare da gabatar da yiwuwar harba makamin da zai rushe cibiyar da Iran take kera makamai masu Linzami dake ƙarƙashin ƙasa.
A lokacin tattaunawar an samu rarrabuwan kai a tsakanin jami'an tsaron Amurka da kuma masu baiwa Trump shawara, har aka tashi ba'a samu matsaya guda daya ba, sai dai an kafa kwamitin da zai duba abubuwan guda uku, kuma an baiwa kwamitin Awanni 20 ya mika rahoton sa.
1. Na farko kwamitin ya duba me yafi dacewa da Amurka, shin harba makamin da zai rushe cibiyar da Iran take kera makamai masu Linzami dake ƙarƙashin ƙasa?
2. Ko kuma Amurka ta shiga Yakin kai tsaye da sojojin ta da kuma kayan aikin ta.
3. Ko kuma Amurka ta nemi a zauna a samu ceasefire wato tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran.
Dalilin da yasa America taki zaban abu daya a nan shine: suna kallon abubuwa guda uku:
1. Na farko suna kallon tarihi, irin yadda America ta kashe kudi a Iraq, Afghanistan da Pakistan a shekarun baya, aka kashe sojojin ta, aka bata lokaci ba tare da an cimma abinda aka je yi ba tun 2003 har 2020.
2. Na biyu, shugabannin tsaron Amurka suna da shakka akan manufar Isra'ila na harba makamin zuwa karkashin kasa, me zai biyo baya tsakanin ta da kawayen Iran irin China, Rasha, North Korea da sauran su, tunda Trump yazo yana so a sassauta alakar da tayi tsami tsakanin America da gwamnatin Joe Biden data gabata.
3.