11/08/2021
cikin soyayya akwai abubuwa da dama wadanda idan masoya s**a yi amfani da su za su kasance farin ciki har ma ayi ko yi da soyayyarsu. Kalmar ‘Gaskiya’ a baki akwai saukin fada amma cikin zuciya da kuma a aikace tana da matukar wahala. Idan aka gina soyayya a tubulin karya, komai daren dadewa sai ta ruguje. A wannan lokacin masoya da dama – ban ce duk ba, domin ba duk aka taru aka zama daya ba – amma dai mafiya yawa duk soyayyar karya ce shi ya sa yaudara take shigowa ciki ba ga mazan ba, ba ga matan ba. Saurayi na son mace, ya yi ta feshe ta da kalaman so da kauna, tun ba ta iya rikewa har ta fara haddace kalamansa tsaf; sai ka rantse da Allah duk duniya babu wata ‘ya mace da yake so sama da ita, kuma a zahiri ba haka ba ne; a wasu lokutan za a iya samun yana da ‘yan matan da yake fadawa irin kalaman sama da goma, burinsa kawai a yi soyayya, ba auren ba; ko kuma soyayya don wani abu. Gaskiya daya ce, idan ka so wata don wani abu nata, wata rana za ka iya rasa wannan abun. Idan ka rasa abin da ya janyo maka soyayyarta shin za ka daina sonta ke nan? Dole ne zuciyarka ta canja a kanta, ka sake kokarin hango wata daban me irin abinda kake so. Ka ga kenan haka za ka dauna cikin hange-hangen da ba zai kare ba, sai ai nazari a yi duba, na san wasu za su halin ai na mata ne ba maza ba, maza ma da nasu domin yanzu su ma sun koya. Ita kuwa budurwa, yayin da ta saka buri a kan lallai sai me wani abu za ta yi soyayyar aure da shi, ranar da ya rasa, shi ke nan an rabu? To ma, ya za ki kasance idan Allah ya mallaka miki shi a matsayin wanda kika aura, daga baya kuma ya rasa abinda k**e so? Dole ne ke ma ki ji canji a zuciyarki. Ga shi kin shiga, yanzu kuma babu damar fita. Haka mace za ta rika tunani a ranta kamar an yaudare ta. Ba kowa ne yake da irin wannan halin ba; wasu na yi, wasu kuma babu ruwansu da hangen lallai sai me wani abun na kawata duniya, burinsu kawai mai addini, tarbiyya, nutsuwa, kamala, sanin ya kamata da kuma sana’a. Sana’ar ma babu ruwansu da lallai sai wat