13/12/2022
IDAN BAKA GANE MENENE ABUNDA SHIEKH ZAKZAKY YAKE CEWA BA KARANTA WANNAN.
Sauda yawa ana wa mutane babarodo da yaudaran kwakwalen su game da da'war Sheikh Ibraheem yaqoub Al-zakzaky.
Wasu s**e: Yana so ya kwace Kasar ne Mulki yadawo hannun sa.
Wasu kuma ; yana so yakafa Aqeedar shi anci ya mallaki mutane.
Gashinan surutai kala kala.
Yana da kyau mugane cewa da hakan ne buƙatun sa da tuni ya tsunduma cikin ƙazamiyar gwamnatin nan da basusan mutuncin ɗan Adamtaka ba. (wa iyazu billah).
Amma zance shine.
Yana da kyau mugane cewa , Ita wannan Duniya ba mu mukayi ta ba . Kuma dai kaman yanda kowa yaganshi yazo darai, haka yake ganin wasu na Mutuwa sukoma basu da rai. Sa anan in muka duba yanda Ranaku ke tafiya cikin tsari ,Iska, wata, misali Rana kullun saita fito babu fashi .haka mukasameta tana fitowa kuma haka ake tafiya abarta.
Wannan kaɗai ya isa kagane cewa akwai wanda yayi ka. ba gwamnatin kasarku tayo kaba, sa anan bakai kai kan kaba.
Sanin cewa ba kai kahalicci kanka ba, kasan akwai wanda yayo ka,Hankalinka ya isa yaba ka cewa, dole yazamo wanda yayo ka ɗinnan yana da Wani tsari nashi da yake son kakasence akai kuma kabi.
Ko shakka babu dukan mu Musulmai da kiristoci kowa yasani cewa akwai ɗan saƙon da Allah yaturo zuwa ga Al ummah .
kuma harmuna iya bada labarin haka.
To Abun tambaya Anan . Shin ƴan saƙon da Uban gijin daya Halicceka yaturo Duniya, Sunyiwa mutane bayani ne akan yanda yakamata abi gwamnatin da take Mulki tana zaluntar mutane ?
Kasani nasani, bahaka s**ace ba.
Sunce ne;
MUGANE ALLAH SHI ƊAYA NE MAHALICCI, WANDA BASHI DA ABOKIN TARAYYA, KUMA SU ƳAN SAƘON SA NE , SUNZO NE DOMIN SU TUNA TAR DAMU NAUYIN DA YAHAU KAN MU, SHINE MUYI WA ALLAH (s.w.t) BAUTA (Muyi masa biyayya aduk abun da yace muyi,sannan muguji duk abun da yace kar muyi).
AKWAI AZABA MAI RAƊAƊI GA DUK WANDA YAƘI BIN UMURNIN SA,DAKUMA MAKOMA NAJIN DAƊI GA DUK WANDA YABI UMURNIN SA.
Idan mai karatu yafahinci wannan Rubutun nasama. Babu ragi babu ƙari shine Shiekh Ibraheem Yaqou