08/08/2019
FALALAR AZUMTAR RANAR ARFA:
:
Daga Othman Muhammad
:
An Ruwaito Daga UWAR MUMINAI AISHAR.A) Ita Kuma Ta Amso Daga ANNABI(S.A.W) Ya Ce:"Hakika a Cikin Aljanna Akwai Wasu Manya-Manyan Gidaje Na Lu'u-Lu'u Da Yaqutu Da Zubarjad Da Zinari Da Azurfa.
;
Sai Na Ce:"Ya MANZON ALLAH Wadannan Gidaje Na Wanene???"
;
Sai Ya Ce:"Na Wanda Ya Azumci RANAR ARFA Ne Ya AISHA! Wanda Ya Wayi Gari a RANAR ARFA Alhali Yana Azumi To ALLAH Zai Bude Mashi Kofofi Talatin Na Alkhairi, Kuma Zai Kulle Mashi 'Kofofi Talatin Na Sharri, Kuma Idan Yasha Ruwa Duk Wata Jijiya Da Take a Jikin Shi Zata Rika Nema Mashi Gafara".
:
Ya ALLAH! Kasa Mu Rabauta Da Wadannan Gidaje Ba Don Halin Mu Ba Don Alfarmar SAYYIDUL-WARA(S.A.W) Ameeeeen.