NBC HAUSA

NBC HAUSA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from NBC HAUSA, Business service, Abuja.

24/12/2022

Yan Majalisar Wakilan Najeriya na shirin yaƙi da dokar cire kuɗi ta CBN

Wasu 'yan Majalisar Wakilan Najeriya sun ci alwashin tilasata wa Babban Bankin ƙasar (CBN) wajen dakatar da shirinsa na rage yawan adadin kudin da 'yan ƙasa da kamfanoni kan cira a kullum, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani daga cikin shugabanni a Majalisar ya faɗa wa jaridar cewa akasarinsu sun aminta cewa ya kamata a jingine dokar baki ɗayanta.

A cikin sabuwar dokar, mafi yawan abin da mutum zai iya cirewa a mako na tsabar kuɗi shi ne naira N100,000, kamfani kuma N500,000. Daga baya aka ƙara ya zama N500,000 ga mutane da kuma 5,000,000.

Tun da farko Majalisar ta nemi CBN ya jinkirta fara amfani da dokar tukunna, wadda za ta fara aiki daga 9 ga watan Janairun 2023, har sai gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana a gabanta.

Sai dai Mista Emefiele bai amsa gayyatar ba yana mai cewa ya fita ƙasar waje don a duba lafiyarsa.

24/12/2022

BREAKING NEWS

Jami'an tsaro sun kashe 'yan fashi 10 a Jihar Kaduna

Jami'an tsaro a Najeriya sun kashe 'yan fashin daji takwas tare da ƙwace babura yayin wani samame da s**a kai a yankin Chikun da Birnin Gwari na Jihar Kaduna, a cewar gwamnatin jihar.

Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun rundunar rundunar haɗin gwiwa na Operation Forest Sanity ne s**a ƙaddamar wa 'yan bindigar cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a.

"Dakarun sun gwabza da 'yan fashin kuma s**a kashe takwas daga cikinsu, sannan s**a ƙwace babura huɗu da wayoyin hannu a samamen farko," in ji shi.

Jami'an tsaron sun sake karawa da 'yan bindigar a karo na biyu kuma s**a ƙwace babur biyu.

A gefe guda kuma, dakarun sun yi nasarar kashe wasu 'yan fashi biyu a yankin Sabon Birni da Maidaro da Dogon Dawa, duka a Jihar ta Kaduna.

A wannan karon ma, jami'an tsaro sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 da kuma harsasai da dama

24/12/2022

Rasha ta gayyaci jakadan Faransa bayan harin da aka kaiwa sojojin Wagner

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta gayyaci jakadan Faransa a birnin Moscow, biyo bayan sakon wani kunshi da ke dauke da bam wanda aka aikawa jami’an kamfanin sojin haya Wagner da ke birnin Bangui Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Bayan faruwar wannan lamari, Rasha ta yi zargin cewa Faransa tana da hannu a harin, zargin da tuni mahukuntan birnin Paris s**a yi watsi da shi.

Moscow ta fada a makon da ya gabata cewa daya daga cikin wakilanta a kasar Afirka ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu.

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta yi watsi da ikirarin da shugaban kamfani Wagner na Rasha, Yevgeny Prigozhin, ya yi na cewa gwamnatin Paris na da hannu, kuma ya kamata a ayyana Faransa a matsayin kasa mai daukar nauyin ta'addanci, inda ta bayyana ikirarin a matsayin farfagandar Rasha.

Rasha ta tabbatar da cewa ta gayyaci jakadan Faransa a Rasha Pierre Levy da wanda ya gabatar da korafi a hukumance kan kalaman da ba su dace ba.

Dakarun Faransa na karshe da aka tura Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun bar kasar a makon da ya gabata bayan dambarwar dangantakar mai karfi tsakanin Bangui da Moscow abin da ya sanya aka tura sojojin Wagner zuwa kasar domin murkushe masu dauke da makamai da s**a addabi kasar.

WHO ta bukaci China da ta kara inganta shirin rigakafin  covid19Wani jami'in lafiya kenan, lokacin da yake daukar samfur...
23/12/2022

WHO ta bukaci China da ta kara inganta shirin rigakafin covid19

Wani jami'in lafiya kenan, lokacin da yake daukar samfuri domin gwajin COVID-19 a Wuhan da ke tsakiyar kasar ChinaAP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci mahukuntan kasar China da su kaddamar da gagarumin aikin yi wa al’umma rigakafi musamman a yankunan da ke fama da cutar covid19.

Shugaban hukumar ta lafiya Tedros Adnom Gebreyesus, ya ce hukumarsa a shriye take domin taimaka wa China ta yaki wannan cuta.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta damu matuka a game da yanayin kiwon lafiya a China, musamman yadda wannan annoba ke dada kamari.

Domin tantance hakikanin abinda ke faruwa, hukumar WHO na bukatar cikakkun bayanai musamman daga asibitoci da sauran hukumomin kiwon lafiya.

"Muna goyon bayan irin matakan da China ke dauka don shawo kan wannan annoba ciki har da shirin fara yi wa jama’a allurar rigakafi a yankunan da annobar ta fi yi wa barazana," in ji Gebreyesus.

"Za mu ci gaba da taimaka wa kasar don jinyar wadanda s**a harbu da kwayar cutar da kuma kare bangaren kiwon lafiya na kasar," a cewar sa.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NBC HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share