11/08/2023
WATARANA ALLAH YA TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWAπ
Shin baka taΙa yin kuka ba a yayin da kake karΙar ran Ζan Adam?
Sai mala'ikan yace:
Nayi kuka sau Ιaya, nayi dariya sau Ιaya sannan na firgita sau Ιaya π’
Sai Allah Yace masa:
Me ya baka dariya ne?
Sai yace: abunda ya bani dariya shine, naje karΙar ran wani mutum sai na iske shi yana cewa mai yi masa takalmi: ka kyautata Ζirar takalman nan, ka Ζira su yadda zan saka su har tsawon shekaru biyar π’
Sai nayi dariya na Ιauki ransa tun bai saka su ba koh sau Ιaya π
Sai Allah Yace masa: toh me yasa ka kuka ya kai mala'ikan mutuwa?
Sai yace:
Abunda ya sakani kuka shine: watarana naje karΙar rayuwar wata baiwar Allah wacce take ita kaΙai a cikin wani babban jeji, da naje sai na iske ta tana haihuwa sai na jira har ta haihu sannan na Ιebe ran nata π
Sai kukan jaririn da na bari a jejin shi kaΙai baya da wanda zai kula shi ya sakani kuka πππ
Sai Allah Yace masa: toh me ya firgitar da kai?
Sai yace: abunda ya firgitar dani shine:
Watarana naje karΙar rayuwar wani malami daga cikin bayin ka sai na iske haske yana fita daga Ζofar Ιakinsa.
Duk lokacin da na kara kusantar Ιakin sa sai hasken nasa ya haska ya mayar dani, sai abun ya firgita Ni π
Sai Allah Yace masa: Ya kai mala'ikan mutuwa shin kasan waye wannan mutumen da hasken sa ya firgitar dakai, kasan waye Shi???
Sai yace: A'a!
Sai Allah Yace masa: Wannan mutumen da hasken sa ya firgitar dakai shine Ζan yaron matar nan da ka Ιauke ranta a jeji ka bar shi shi kaΙai bbu mai kula dashi βοΈ
Na kula dashi, na bashi kariya har ya zamo abunda ya firgita βοΈ
LA ILAHA ILLALLAH πππ
TABBAS SHA'ANIN UBANGIJI DABAN YAKE π
YA UBANGIJI KAYI MANA SAUQIN FITAR RAI πππ
YA ALLAH KA KULA DAMU KUMA KA SHIGA LAMURAN MU KAMAR YADDA KA SHIGA LAMURAN WANNAN JINJIRIN πππ
Idan labarin yayi tasiri a gareka kaima kayi sharing saboda 'yan uwa su amfana π