18/08/2026
Jami'ar jihar Kaduna KASU ta Karyata Ikirarin ASUU Na Cewa Malamai 200 Sun Yi Murabus.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Prof. Abdullahi Ibrahim Musa, ya musanta ikirarin ASUU-KASU na cewa malamai 200 sun yi murabus daga jami’ar saboda rashin kyawun yanayin aiki.
VC ɗin ya ce wannan ikirari ba shi da tushe a bayanan jami’ar, yana mai cewa sauyin ma’aikata sakamakon murabus, ritaya, sauyin aiki ko neman wasu damar sana’a abu ne da ya saba faruwa a jami’o’i.
Ya kalubalanci ASUU da ta gabatar da hujjoji masu inganci, ciki har da sunayen malaman da ake cewa sun yi murabus, ranar da s**a yi murabus da kuma dalilan barin jami’ar.
Prof. Musa ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta kashe sama da ₦800m wajen jin daɗin ma’aikata cikin shekaru uku, sannan ta biya ₦146m na albashin da aka riƙe da wasu alawus-alawus da aka gada daga tsoffin gwamnatoci.
Ya kuma ce an kafa tsarin tallafin ₦50m duk wata tsakanin gwamnatin jihar, shugabancin jami’a da ASUU-KASU domin tallafa wa jami’ar.
A shekarar 2026 kaɗai, gwamnatin jihar ta kuma fitar da sama da ₦200m don gudanar da ayyukan jami’ar, yayin da sama da ₦300m aka zuba wajen tantancewa da sabunta akrediteshin na shirye-shiryen karatu.
VC ɗin ya ƙara bayyana cewa KASU ta kafa cibiyoyin bincike 14 da cibiyoyi na musamman guda biyu, tare da samun tallafin bincike na ƙasa da ƙasa guda bakwai cikin shekaru uku.
Ya ce jami’ar ta kuma samu ₦1bn TETFund domin aikin noma na kasuwanci, yayin da rage kuɗin makaranta da gwamnatin Uba Sani ta yi a jami’o’in jihar ya taimaka wajen rage wa iyaye da ɗalibai nauyin kashe kuɗi.
Prof. Musa ya amince cewa har yanzu akwai wasu matsalolin jin daɗin ma’aikata da ba a warware su ba, amma ya ce gwamnati da jami’a na ci gaba da magance su.
Ya roƙi ASUU-KASU da ta guji duk wani mataki da zai kawo cikas ga karatun ɗalibai, yana mai jaddada cewa tattaunawa da fahimtar juna ne hanya mafi dacewa wajen warware matsalolin ma’aikata, yayin da yajin aiki ya kamata ya zama matakin ƙarshe.
Yanzu dai tambayar ita ce: Shin ASUU za ta fito da sunayen malaman 200 da ta ce sun yi murabus, ko kuma za a ci gaba da musayar zarge-zarge tsakanin ɓangarorin biyu?