20/12/2018
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN KATSINA RT. HON, AMINU BELLO MASARI DA MAI MARTABA SARKIN KATSINA ALH (DR) ABDULMUMIN KABIR USMAN
INA MAFITA GA TADA KASUWAR YAR'KUTUNGU
Assalamu Alaikum
Bayan gaisuwa da jin jina ga shuwaga bannin mu masu Albarka.
Ko shakka babu kowane shugaba yanasan cigaban al ummar shi, kuma babu wani shugaba mai aldaci da zaiso cibaya da kuma tabar-barewar tattalin arzikin al ummarshi.
ko shakka babu kasuwar yarkutungu kasuwa ce mai da dadden tarihi sama da shekara hamsin ana cinta, kuma kashi sittin na yan kasuwan yan asalin karamar hukumar katsina ne, yayinda kashi talatin suna zowa daga kananan hukumomi na jihar katsina kamar su kaita, jibia, batsari, matazu, dutsinma da sauran su, kuma kashi goma suna zowa ne daga kano, jigawa da jamhuriyar nijar.
sannan mafi yawancin yan kasuwar dalibai ne wadanda sungama karatu basu samu aiki ba, wasu nada Bsc, N c e, Hnd da Msc, Nd da Ssce. sai kuma manoma wa yanda idan sunyi noma suke kawo amfaninsu su sayar. kuma wa yanda ke cin kasuwar sun kai adadin mutun dubu Ashirin da biyar.
SUWA SUKE SO ATADA KASUWAR??
wasu tsirarun mutane wa yanda basu kai kashi biyu ckin dari ba sune suke so atada ta
MINENE MANUFARSU??
manufarsu itace idan gwamnati tabada sabon fili suci karensu ba babbaka kamar yanda muka gani kashi tamanin na wa yanda akaba ba yan kasuwan yar kutungu bane masu hannu da shuni ne.
MINENE MANUFARMU?
Babu tayadda za'ai mutun ya auro mata sai ranar tarewa wani yazo yace shi yafi angon sanin abinda za'ai adakin don haka yabarshi su kwana tare,
kowa ya sani kasuwa yan kasuwane ke cinta, idan hakane to mizai sa aba wasu runfuna ba yan kasuwan ba, MUFA manufarmu itace afadada mana kasuwarmu ba atada ta ba, saboda kowa yasan matsalar tada kasuwa, Dolene idan aka tada kasuwa mafiyawanci sai yan kasuwa sun durkushe kamar yadda muka gani ga tsohuwar kasuwa da kuma kasuwar yan gwari da kayawa dakuma kasuwar daura
KIRANMU GA GWAMNATI DAKUMA MASARAUTA
muna rokon wannan gwammati tatai maka tabarmu muci gaba da kasuwancin mu inda muka saba, kuma ta fadada mana ita domin hakan shine hanya mafita, saboda inda ake cewa za'a maidamu babu tsaro agurin kuma ba ruwa ba wuta agurin kuma gurin yayi mana kadan bai kai daya bisa hudu na inda muke ba, kuma muna kira da adaina daukar maganar munafukai masu san cigaban kansu arinka daukar maganar masu san cigaban jama'a, munfatan za'a karbi kokenmu
Rubutawa
Isah Musa Daura
undergraduate Bsc Chemistry Umaru musa Yar'adua university