31/05/2026
🚨 GAME DA SIDRA 🚨
Idan kasan ba dogon holding za ka yi ba, bana baka shawarar ka sayi Sidra a wannan lokacin.
Farashinta ya riga ya tashi sosai. Duk da akwai yiwuwar ta ƙara hawa, amma masu son shiga su fita cikin gajeren lokaci su yi hattara.
Ka tuna, a kasuwar crypto ana samun riba ne idan ka saya lokacin da farashi yake ƙasa, ka sayar lokacin da ya tashi.
Amma idan ka bi FOMO da son shiga saboda mutane suna magana a kai, sau da yawa za ka saya da tsada sannan ka sayar da araha.
Duk coin ko token da za ka saya, ka fara yin bincike a kansa kafin ka saka kuɗin ka.
Daga ƙarshe, idan akwai wanda ya sayi Sidra tun tana ₦40, ya kawo mana mu saya a ₦74 mu ba shi kuɗin sa. 😄💰
*Musa Fullo Azare ✅*