Ina masoya

Directions Website

Ina masoya Sharadi baa maganar batsa anan

KADA KASUWAR BOGE TAJEFA MUTUM A ILLAR DA ZAIKASA FIDDA KANSHI
24/08/2026

KADA KASUWAR BOGE TAJEFA MUTUM A ILLAR DA ZAIKASA FIDDA KANSHI

Happy MAULUD
18/08/2026

Happy MAULUD

Watch, follow, and discover more trending content.

17/08/2026

Watch, follow, and discover more trending content.

11/06/2026

I got over 20 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

*TAKAITACCEN BAYANIN JADAWALIN ZABEN 2027 NA INEC*Wannan jadawali ya fara ne daga *30 ga Mayu, 2026* kuma ya raba zaben ...
11/06/2026

*TAKAITACCEN BAYANIN JADAWALIN ZABEN 2027 NA INEC*

Wannan jadawali ya fara ne daga *30 ga Mayu, 2026* kuma ya raba zaben gida biyu:

*1. Zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya*
- *26 ga Yuni, 2026*: Jam’iyyu za su karbi lambobin shiga shafin INEC a Abuja.
- *27 ga Yuni – 11 ga Yuli, 2026*: Za a bude shafin yanar gizo domin loda takardun ‘yan takarar Shugaban Kasa da Majalisa.
- *15 ga Agusta, 2026*: INEC za ta fitar da sunayen ‘yan takara na karshe.
- *25 ga Agusta, 2026*: Ranar karshe da za a iya janye ko sauya dan takara.
- *23 ga Satumba, 2026*: Fara yakin neman zabe.
- *15 ga Janairu, 2027*: Kammala yakin neman zabe da tsakar dare.
- *16 ga Janairu, 2027*: *Ranar zabe*.

*2. Zaben Gwamna da na Majalisar Jiha*
- *18 ga Yuli – 8 ga Agusta, 2026*: Za a loda takardun ‘yan takarar Gwamna da Majalisar Jiha.
- *24 ga Satumba, 2026*: Ranar karshe ta janye ko sauya dan takara.
- *6 ga Oktoba, 2026*: INEC za ta fitar da sunayen ‘yan takara na karshe.
- *2 ga Disamba, 2026*: Fara yakin neman zabe.
- *4 ga

MARA GASKIYA KO ARUWA? DA DUMI-DUMI: Na Girgiza Matuƙa Da Aka Ba Da Umarnin K**a Ni — Inji Mele KyariDaga Ayau News // S...
11/06/2026

MARA GASKIYA KO ARUWA? DA DUMI-DUMI: Na Girgiza Matuƙa Da Aka Ba Da Umarnin K**a Ni — Inji Mele Kyari

Daga Ayau News // Sadiya Yusuf

Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya ce ya girgiza matuƙa da aka Bada umarnin k**a shi da Majalisar Dattawa ta bayar.

Ya ce yana ƙasar waje domin jinya, kuma ya riga ya sanar da kwamitin binciken hakan tun da farko.

Kyari ya jaddada cewa bai guje wa binciken ba, kuma yana shirye ya ba da cikakken haÉ—in kai da zarar ya dawo Najeriya.

Mezakuce?

LIKE // SHARE & FOLLOW ~Ayau News

YAKIN AHZAB (wanda kuma ake kira da Yakin Khandak ko Yakin Gidaje) yana daya daga cikin mafi muhimmanci da ban mamaki a ...
07/06/2026

YAKIN AHZAB (wanda kuma ake kira da Yakin Khandak ko Yakin Gidaje) yana daya daga cikin mafi muhimmanci da ban mamaki a tarihin Musulunci. An yi wannan yaki ne a cikin watan Shawwal na shekara ta 5 bayan Hijira (wanda ya yi daidai da watan Fabrairu ko Maris na shekara ta 627 Miladiyya).
Ga takaitaccen tarihin yakin da yadda ya auku:
1. Dalilin Yin Yakin (Dalilin Sunan)
Ahzab (Gamayyar Runduna): Sunan "Ahzab" yana nufin "kungiyoyi" ko "gamayya". Hakan ya faru ne saboda Yahudawan Banu Nadir (wadanda Manzon Allah (SAW) ya kora daga Madina saboda barna da cin amana) sun hada baki da kafiran Quraisawa na Makka da sauran kabilun Larabawa k**ar su Gatafan. Sun hada babbar runduna ta mutane kusan 10,000 da nufin su karkashe Musulmai gaba daya su ruguza Madina.
Khandak (Guba/Rami): Ana kuma kiran yakin da Yakin Khandak saboda dabarar da Musulmai s**a yi ta gina rami mai fadi da zurfi don kare birnin Madina.
2. Dabarar Salman al-Farsi (RA)
Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya sami labarin cewa runduna mai girma tana tafe, ya tara sahabbansa don yin shawara (Shura). A nan ne sahabi Salman al-Farsi, wanda dan asalin kasar Farisa (Persia) ne, ya ba da shawarar da Larabawa ba su taba saninta ba: gina babban rami (Khandak) a arewacin Madina, inda yake da fili kuma abokan gaba za su iya biyo wa. Sauran bangarorin Madina kuwa suna da kariya ta dabi'a ta dtswatsu (Harrah) da kuma gidajen bishiyoyin dabino.
Manzon Allah (SAW) ya karbi wannan shawara, kuma Musulmai kusan 3,000 s**a tashi tsaye, ciki har da Manzon Allah da kansa, s**a raba korafe-korafe s**a tona ramin cikin kwanaki kadan kafin makiya su iso.
3. Kewaye Madina (The Siege)
Lokacin da dakarun Ahzab s**a iso, sun yi mamakin ganin ramin gudanarwa, domin dabarar yaki ce da ba su taba gani ba. Ba su da damar tsallakowa da dawakansu. Saboda haka, sai s**a kafa sansani s**a kewaye Madina na tsawon kwanaki kusan 20 zuwa guda 30.
A lokacin da ake wannan takaddama, Musulmai sun shiga cikin matsananciyar fargaba da yunwa da sanyi. Alkur'ani ya siffanta wannan lokaci a cikin Suratu Al-Ahzab, inda yake cewa zukata sun tashi har sun kai ga makogwaro saboda tsananin tsoro, kuma munafukai sun fara bayyana kansu.
4. Cin Amanar Banu Quraiza
Abubuwa sun kara tsananta lokacin da Yahudawan Banu Quraiza, wadanda ke zaune a cikin Madina kuma suke da yarjejeniyar kare birnin tare da Musulmai, s**a karya alkawari. Shugaban Banu Nadir (Huyayy bin Akhtab) ya zuga su, s**a amsa kiran dakarun Ahzab cewa za su farmaki Musulmai ta baya (ta inda iyalansu suke). Wannan ya sanya Musulmai cikin hadari ta kowane bangare.
5. Wayon Yaki na Nu'aim ibn Mas'ud
A cikin wannan mawuyacin hali, wani babban mutum daga kabilar Gatafan mai suna Nu'aim ibn Mas'ud ya zo wajen Manzon Allah (SAW) ya ce ya karbi Musulunci a asirce, kuma mutanensa ba su sani ba. Manzon Allah (SAW) ya gaya masa cewa "Yaki dabarace", don haka idan da akwai yadda zai yi ya raunana gwiwar abokan gaba, ya yi.
Nu'aim ya yi amfani da hikima:
Ya tafi wajen Banu Quraiza ya ce musu Quraisawa za su iya gajiyawa su koma Makka su bar su, don haka kada su taya su yaki har sai Quraisawa sun ba su wasu manyan mutanensu a matsayin jingina (garkuwa).
Sannan ya tafi wajen Quraisawa da Gatafan ya gaya musu cewa Banu Quraiza sun yi nadamar abin da s**a yi, kuma sun kulla yarjejeniya da Muhammad cewa za su k**a wasu manyan mutanen Quraisawa su mika masa don ya kashe su a matsayin tubansu.
Wannan ya sanya shakku da rashin amon juna tsakanin dakarun Ahzab da Yahudawan Banu Quraiza, hadin gwiwarsu ta ruguje.
6. Taimakon Allah da Karshen Yakin
Yayin da Musulmai s**a dage da addu'a (inda Manzon Allah ya yi addu'ar: "Ya Ubangijin da ke saukar da Littafi, Mai saurin bincike, Ka gurgunta rundunonin nan"), Allah Madaukakin Sarki ya aiko da taimakonsa:
Guguwa mai tsanani: Allah ya aiko da wata iska da sanyi mai tsanani da daddare, wadda ta karkatar da tukwanensu na girki, ta tumfuke tantunansu, ta tsorata dawakansu, ta kashe wutarsu.
Mala'iku: Allah ya aiko da rundunar Mala'iku wadanda s**a jifa tsoro a zukatan kafirai.
Ganin haka, shugaban Quraisawa, Abu Sufyan, ya ba da umurnin cewa kowa ya tattara ya koma gida. Haka rundunar Ahzab ta watse ba tare da sun yi nasarar komai ba.
Muhimmancin Yakin
Wannan yaki ya zama babban juyi a tarihin Musulunci. Bayan yakin ya kare, Manzon Allah (SAW) ya ce: "Yanzu mu ne za mu kai musu hari (Makka), ba su ba kuma da za su zo gare mu." Kuma hakan ce ta faru, domin bayan wannan yakin, ikon Quraisawa ya fara raguwa har ya kai ga can aka bude garin Makka (Fath Makka).

KUNJI TSIYAR AUREN MAYYAR WAYA
05/06/2026

KUNJI TSIYAR AUREN MAYYAR WAYA

Nidai huummmm@
05/06/2026

Nidai huummmm@

05/06/2026

SANARWA TA MUSAMMAN!

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa watau (INEC), Reshen Karamar Hukumar Bakori, na Sanar da jama’a cewa an shiga zango na uku, wanda shi ne zango na Karshe na aikin yin Rijista katin Zabe.

A KULA: Idan aka kammala wannan zango na uku, ba za a Kara yin Rijista ba sai bayan shekaru 3 ko 4 masu zuwa.

Don haka, ana kira ga duk wanda ya fada cikin wadan nan Rukunonin Mutanen da za'a zayyano a Kasa to yayi Gaggawar zuwa OFISHIN INEC:
1. Wanda ya kai Shekaru 18 a yanzu.
2. Wanda katin Zabensa ya Bace.
3. Wanda Katinsa ya lalace ko ya goge.
4. Wanda ke son canza Rumfar zabe; da sauran su.

Duk wanda ya kasance Daya daga cikin wadan nan Mutanen, yazo Ofishin INEC da ke KASUWAR SAMA BAKORI, kusa da Ofishin ‘Yan Sanda na Bakori, domin yin RIJISTA.

Ku taimaka ku sanar da sauran jama’a tare da tunatar da su cewa.

KURIARKU, ‘YANCINKU.

Address

Bakori

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ina masoya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share