14/05/2021
...
Imamul Bukhari asalin sunansa shine
Muhammad bin Isma’il bin Ibrahim bin
Mugira, Abu Abdullah, Al-Ju’ufi , Ana masa
kirari da Malamin Malamai na duniya face
Malamin sa ( Imam Malik ) , kuma jagora wajen
sanin fiqihun hadisi, yayi karatu a wurin
malaminsa wato Babban Malamin nan Imam
Malik Ibn Anas . An haifi Imamul Bukhari ranar
Juma’a sha uku ga watan Shauwal shekara ta
(194A.H), mahaifinsa ya rasu tun yana yaro,
don haka ya taso a karkashin kulawar
mahaifiyarsa. Imamul Bukhari ya kasance a
lokacin da yake yaro ya samu matsala a
ganinsa sai ya zamanto ba ya gani,wata rana
mahaifiyarsa sai ta yi mafarki da Annabi
Ibrahim (AS), sai ya ce mata: Allah ya
dawowa da danki ganinsa, da gari ya waye sai
taga idon danta ya bude. Allah ya yiwa
imamul Bukhari baiwa ta haddar hadisai,
harma ana hikaito cewa ya haddace hadisai
(70,000) tun yana dan shekara (16), shi yasa
wani daga cikin malamai yake cewa: duk
hadisin da Imamu Bukhari bai san shi ba, to
ba hadisi ba ne, har wasu Malamai ma suna
gabatar da shi a wajen sanin hadisi da fiqihun
hadisi a kan imam Ahmad da Ishaq. Imam
Muslim ya yi karatu a wajensa.