28/04/2025
IJMA'IN MALAMAI A KAN MAKOMAR IYAYEN ANNABI (SAW)
Asali tun farko babu sabani a kan makomar iyayen Annabi (saw), saboda kowa ya san cewa; ba su mutu a kan imani ba. Kuma “Ahlul Jahiliyya” ba “Ahlul Fatra” ba ne. Don haka hukuncin wajabcin Imani yana kansu, wadanda s**a mutu a cikinsu ‘yan wuta ne, kamar yadda al-Qarafiy ya hakaito Ijma’in Malamai a kan haka, ga shi kamar haka:
"حكاية الخلاف في أنه عليه الصلاة والسلام كان متعبدا قبل نبوته بشرع من قبله، يجب أن يكون مخصوصا بالفروع دون الأصول، فإن قواعد العقائد كان الناس في الجاهلية مكلفين بها إجماعا، ولذلك انعقد الإجماع على أن موتاهم في النار يعذبون على كفرهم، ولولا التكليف لما عذبوا، فهو عليه الصلاة والسلام متعبد بشرع من قبله".
شرح تنقيح الفصول (ص: 297)
Haka Ibnul Jauziy ya hakaito Ijma’i a kan Iyayen Annabi (saw) ba Muminai masu shiga Aljanna ba ne, inda ya ce:
"لا يختلف المسلمون أن عبد المطلب مات كافرا، وكان لرسول الله صلى الله عليه وسلم يومئذ ثمان سنين.
وأما عبد الله فإنه مات ورسول الله صلى الله عليه وسلم حمل، ولا خلاف أنه مات كافرا. وكذلك آمنة ماتت ولرسول الله صلى الله عليه وسلم ست سنين.
فأما فاطمة بنت أسد فإنها أسلمت وبايعت ولا تختلط بهؤلاء".
الموضوعات لابن الجوزي (1/ 283)
Abin da zai tabbatar maka da wannan Ijma’i shi ne Malaman Hadisi suna kulla babi wa Hadisan makomar Iyayen Annabin (saw) da tarjamomi kamar haka:
(1) Ibnu Majah ya ce:
"باب ما جاء في زيارة قبور المشركين".
سنن ابن ماجه ت الأرنؤوط (2/ 512)
"Babin Hadisan da s**a zo a kan ziyarar kabarburan mushrikai".
A cikin wannan babi, Hadisi na farko da ya ruwaito shi ne Hadisin ziyarar kabarin mahaifiyar Annabi (saw).
(2) Al-Nasa’iy ya ce:
"زيارة قبر المشرك"
سنن النسائي (4/ 90)
"Ziyarar kabarin mushriki".
Shi ma Hadisi na farko da ya ruwaito a wannan babin shi ne Hadisin ziyarar kabarin mahaifiyar Annabi (saw).
(3) Ibnu Sunniy ya ce:
"باب ما يقول إذا مر بقبور المشركين"
عمل اليوم والليلة لابن السني (ص: 546)
"Babin abin da mutum zai fadi idan ya zo wucewa ta kabarburan mushrikai".
A wannan babin sai ya ruwaito Hadisin da Balaraben kauye ya tambayi