22/08/2026
Rayuwa bada tabbas. Yau kana da ƙarfi, gobe ba ka san abin da zai faru ba. Kada ka bari neman abin duniya yasa ka manta da Allah da kuma abin da zai amfane ka bayan mutuwa.
Ka kyautata wa mutane, ka yafe, ka taimaki wanda yake buƙata, kuma ka yi amfani da lokacinka wajen abin da zai amfani rayuwarka da kuma lahirarka.
Ka tuna: duk abin da kake da shi aro ne. Wata rana za a tambaye ka yadda ka yi amfani da shi.
Allah Ya sa mu rayu cikin alheri, Ya sa ƙarshen rayuwarmu ya zama mai kyau. Ameen.