14/02/2023
KAURAN GWANDU NEW MEDIA INITIATIVES.
Motto:- Promoting Good Government and Community Development.
Jahar Kebbi ta Jima tana neman Irin Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu AMATSAYIN Gwamnan Jahar Kebbi tun dawowar Demokradiyya a 1999 masu irin tunanin sa suke suna neman Jagorancin Jahar Kebbi Allah bai basu ba.
Sai Gashi Kwatsam Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya sake Yunqurowa da Qarfin Allah inda Alkaluma sun nuna cewa in Shaa Allahu wannan Karon Haqar mu zata cimma ruwa wajen Zaben sa amatsayin Gwamnan Jihar Kebbi ranar Assabar 11/03/2023.
Yaku Matasan Jahar Kebbi Kuyi Kokarin Ganin Cewa kun bada taku Gudummawa wajen Kafa Gwamnati mai Inganci ta tasiri agurin Al'umma.
Kuri'ar ka nada muhimmanci sosai don Ganin wannan Guri na Al'umma nagartatta ta cika.
Amatsayin ka na Matashi Kuri'ar ka daya 1 ba qaramin muhimmanci Gareta ba a wannan karo, idan zaka iya bada Kuri'a daya akwai Buƙatar ka nemo Mutane ukku 3 da kake da tabbacin zasu bada tasu kuri'a ga Zaben Malamin Makaranta mai kishin Ilimi da cigaba Jahar Kebbi.
Da kuri'u ukku 3 Ukkun nan masu inganci zamu iya kafa Gwannati in Shaa Allahu.
Samun irin su Hon Kabiru Labbo Jega FCNA AJIYAN JEGA GWARZON GWANDU akusa da Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu zai gamsar da Al'ummar Jahar Kebbi cewa Kauran Gwandu zai baiwa maradda kunya bayan yakafa Gwannati.
Allah katausaya muna kabaiwa Kauran Gwandu nasara da Rinjaye a zaben watan Gobe.
Naku
Yahuza Zaki Gwandu
Chairman K.G.N.M.I.
Talata 14/02/2023.