15/04/2025
Ka Manta da Buri Ka Gina Tsari..
Mutane da yawa suna da buri. Buri iri-iri.
Wani zai ce, “Zan zama attajiri.”
Wani ya ce, “Zan zama jarumi.”
Buri fa abu ne mai sauƙin furtawa, amma wahalar aikatawa.
Gaskiyar magana ita ce: buri ba ya kai mutum ga Nasara sai dai Tsare-tsaren da ka shirya su kai ka ga Nasara.
Idan kana da buri ba tare da tsari ba, kamar kana da irin Shuka ne a hannu amma baka yi shukar ba kaga sai dai kayi ta kallon irin ba zai amfaneka da komai ba.
Wata rana, wani yaro ya zo wajen Malam Yaro ya ce:
– “Malam, ina da buri zan zama mutum mai ƙarfi kuma Jarumi.”
Malam ya ce: “To me kake yi dan kaga burinka ya cika ?”
Yaron ya ce: “Ina Bacci da rana, in ci tuwo da daddare.”
Malam ya ce: “ba zaka taɓa zama jarumi ba kuwa, sai dai ka zama jarumin barci!
Me ake nufi da tsari?
Tsari shi ne al’adar da kake maimaitawa kullum, abubuwan da ko yaushe kake mai-maitawa. Ɗabi'ar da kake mai-maitawa wannan ita ce tsari kuma ita ce kawai zata Kai ka ga cikar burinka.
“Scott Adams ya ce: Buri shine abin da kake so ka samu. Tsari kuma shi ne yadda za ka kai ga samun abun.”
Tsari dai shi ne kashin bayan buri.
Ba ka buƙatar ka ce wa duniya “zan yi” — ka fara yi, koda ƙalilan ne.
– Idan kana son rage kiba, kada ka fara da “zan daina shan sukari har abada.”
Ka fara da: “Zan rage kwalbar lemo daga uku zuwa ɗaya.”
– Idan kana son zama mai kudi, kada ka ce “zan tara miliyan goma cikin shekara.”
Ka ce: “Zan adana ₦1000 duk mako ba tare da fashi ba.”
Idan kana son Ƙwarewa a harshen Turanci, ka ce: “Zan koyi sabuwar kalma ɗaya duk rana.”
Wannan tsarin da zaka tsara wanda zaka aiwatar kullum shine Nasara kuma shine cika burin don haka mayar da hankali akansa da tabbatar da shi mafi wahala kuma shine mafi muhimmanci fiye da burin.
A ƙarshe, ka sani...
Buri kalma ce. Tsari aiki ne.
Buri yana zaune a zuciya. Tsari yana motsa ƙafafu.
Buri yana jin daɗin faɗi. Tsari yana jin daɗin aiki.
Idan kana so ka canza rayuwa, kar ka ƙara kafa manufa kai kaɗai – sai ka kafa tsari mai sauƙi, ka tsaya kai da shi har ya zama jiki.