Arewa Daulan Shehu Dan Fodiyyo

Arewa Daulan Shehu Dan Fodiyyo Wannan shafi tana nufin fahimtar DA yan arewa asalinsu ne DA kuma nuna wajibcin hadakai don't tinkaran matsalolin dake tinkaran yankin

21/10/2021

Hakika mune musulmai kuma mune muke zaune a yankin arewa yankin da turawan mulkin mallaka s**a sami iyaye da kakannimu da tsari shugabancin musulunci da tsari zamantakewa da kasuwanci! A takaice bature ya samu yankin arewa cibiya kuma sashin daular shehu usman dan fodiyo da dukan k**ala na yadda mutun ya dace ya rayu. Amma yaya akayi ayau wannan yanki ta arewa ta zama mafi munin yanki da dan adam ke rayuwa a ciki? Wa zai fara amsa mana wannan tambaya namu?

28/09/2020

Ta Yaya alummar musulmi zasu tsamar da kasan daga irin mummunan halin da ake ciki a kasar nan musamman a yanking Areww

25/10/2019

TARIHI DA JIHADIN SHEHU USMAN DAN FODIYO
Asalin sa da kabilarsa
Shehu asalinsa Bafulatani ne da aka haifa a Maratta a cikin kasar Gobir a ranar
15 Disamba, 1754 Miladiyya. Sunan mahaifinsa Muhammadu Fodiyo. Asalinsu
Fulani ne mutanen Futatoro a cikin kasar Senegal.
A wajen karni na 15 kakanninsa s**a yo kaura daga Futatoro s**a zo kasar
Hausa a zamanin Sarkin Kano Yakubu. Kakansa shi ne Musa Jaffolo, yana daga
cikin ayarin da s**a zo kasar Hausa. Sun farzama cikin birnin Kwanni wanda ke
cikin Jamhuriyar Nijar ta
yau. Yawanci malamai ne masu ba da karatu, sannan kuma suna karantarwa
haka kuma suna ɗaukar karatu a inda s**a samu malamai. Wani lokaci su kan
yi aiki a fadar Sarakai ko su rika koyar da ‘ya’yan Sarakai ilimi. Suna da yawa
kuma sun bazu kusan ko’ina a kasar Hausa.
Shehu ya yi karatu a wajen Mahaifinsa da kuma kawunsa, daga nan
ya yi karatu a wajen malamai masu yawa a wurare daban-daban.
Daga cikin muhimman malamansa akwai Malam Jibirila na Agadas
wanda ake zaton daga gare shi ne Shehu ya samu tasirin yin jihadi,
domin Malam Jibirila ya yi kokarin yin jihadi a kasashen Buzaye.
Shehu ya yi yawo da dama, bayan ya dawo gida sai ya k**a yin
wa’azi da karantarwa a wurare irin su Gobir da Kebbi da Zamfara.
A wannan lokacin ya samu kasar Hausa na yin wasu abubuwa na
al’adun gargajiya, k**ar su bori da tsafi da haɗa Musulunci da
al’adun gargajiya, saboda haka Shehu ya yi tinanin aiwatar da jihadi
don ya kawar da al’adun gargajiya daga gurɓata addinin Musulunci.
Haka kuma akwai zalinci mai yawa tsakanin Sarakuna. Duk irin
waɗannan abubuwan ne s**a harzika Shehu ya sa ya yi jihadi don a
daina cuɗanya Musulunci da al’adun Maguzanci, a daina zalunci da
danne wa talakawa ‘yancinsu, a kuma daina nuna bambanci wajen
shari’a.
Wannan ya sa ya samu goyon bayan talakawa da dama, domin irin
zalincin da Sarakuna suke yi musu.
A lokacin Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo wannan wa’azin na Shehu
ya yi tasiri gare shi, don haka ya yi ‘yan gyare-gyare a fadarsa, ya
rage haraji ya kuma umarci maza Musulmi suke yin rawani, mata
kuma suke yin lilliɓi, kana Shehu ya zama Malamin ‘ya’yansa. Irin
wannan sassauci da Bawa ya yi, Fadawa ba su ji daɗin sa ba, domin
an toshe musu waɗansu hanyoyi na samu. Ran ‘yan-bori ya ɓaci
ganin an kara wa Musulunci daraja.
Bawa ya rasu a 1796 Miladiyya, sai kaninsa Nafata ya gaje shi, da
hawansa sai Fadawa da ‘yan-bori s**a kara zuga shi, don haka sai
ya soke sassaucin da Bawa ya yi, ya kara haraji aka kuma cigaba da
zalinci. Nafata ya ba da umarnin duk wanda bai gaji Musulunci ba,
karda ya shiga wanda ya shiga kuma ya fita.
Nafata bai daɗe ba ya rasu a 1802. Bayan ya mutu, sai ɗan Bawa
wato Yumfa ya gaje shi. An zaci za a samu kyakkyawan sassauci a
wurin Yumfa domin shi ɗalibin Shehu ne, to amma sai abun ma ya
kara ta’azzara, zigar Fadawa da ‘yan-bori ta kara karfi. Ya hana mata
lilliɓi ya hana maza kuma sanya rawani, sannan ya takurawa duk
wanda aka ji yana goyon bayan Shehu Usman Danfodiyo.
A shekarar 1804 , Shehu ya yi hijira daga ‘Dagel ya koma Gudu shi da
Almajiransa. A kan hanyarsu Almajiran Shehun s**a yi mishi Sarkin
Musulmi, kaninsa Abdullahi Fodiyo da ɗansa Muhammadu Bello aka
yi musu Sarakunan yaki.
Bayan Shehu ya koma Gudu, sai mutane s**a dinga biyo shi, ganin
haka sai Sarkin Gobir Yumfa ya yi kokarin hanawa, ya umarci
Sarakunansa da kada su bar kowa ya yi kaura zuwa wurin Shehu.
Daga nan s**a shiga cika aiki, s**a rika k**a mutanen Shehu suna
azaftar da su, suna kwace musu dukiyoyi amma wannan bai hana
mutane zuwa wurin Shehu ba. Da Yumfa ya ga haka, sai ya ɗaura
yaki da Shehu a shekarar 1804 , ya samu Shehu a Gudu aka fara yaki
a Tafkin Kwatto inda Shehu ya yi nasara. Aka cigaba da yaki har
zuwa shekarar 1808.
Bayan birnin Alk’alawa ya faɗi, sai sauran kasashen Hausa s**a
mika wuya, inda Shehu Usman Danfodiyo ya dinga ba da izini ko tuta
ga Malaman da zasu mulki waɗannan kasashen, waɗanda daga
bisani aka koma kiran kasashen tare da Malaman da aka damka wa
tuta da “Tutocin Shehu.” Wato su ne k**ar haka:
TUTOCIN SHEHU.
1. Kano- Malam Suleman.
2. Katsina- Malam Umarun Dallaji.
3. Katagum- Malam Ibrahim Zaki.
4. Kazaure- Malam Dantunku.
5. Bauchi- Malam Yakubu.
6. Daura- Malam Isiyaku.
7. Adamawa- Malam Moddibo.
8. Hadeja- Malam Sambo.
9. Misau- Malam Goni Muktar.
10. Gombe- Malam Buba Yero.
11. Ilorin- Malam Abdul’alim.
12. Zazzau- Malam Musa.
An riga an fara bayyanawa a baya kaɗan cewa, Shehu Usman
Danfodiyo ya yi jihadi a kasar Hausa baki ɗayanta, inda daga bisani
ya kafa daula mai karfi a karkashin cikakken shugabancinsa. An gina
wannan daula ne bisa tsari mai inganci da adalci da kyautata ɗabi’u
da halayen jama’a. (Galadiman Daji; 2008: 5)
Shehu Usman Danfodiyo ya rasu a ranar 20 Afrilu, 1817.
IYALAN SHEHU.
Matansa:
■ Maimuna.
■ Aisha.
■ Hauwa’u.
■ Hadiza.
‘Ya’yansa:
Daga cikin ‘ya’yan Shehu Usman Danfodiyo guda 23, akwai:
■ Muhammad Bello.
■ Nana Asma’u.
■Abu Bakr Atiku.
■ Sunan Mahaifiyarsa Maimuna.
■ Sunan Mahaifinsa Mallam Muhammadu Fodiyo.
■ Sunan kaninsa Abdullahi Danfodiyo.
KAMMALAWA.
A cikin wannan rubutun, an tsakuro wani abu ne daga cikin rayuwar
Shehu Usman Danfodiyo, an tattauna a kansa. Tarihin Shehu Usman
kogi ne mai matukar girma da faɗi.
Share

Wait ke nan ba AREWA bane ki shiga hankalinki. My muna kishin al'umarmu ba k**ar yan AREWA masu murnan kashe yan uwansu
10/08/2019

Wait ke nan ba AREWA bane ki shiga hankalinki. My muna kishin al'umarmu ba k**ar yan AREWA masu murnan kashe yan uwansu

05/04/2019

Barkan mu juma'a al'umman arewacin nigeria! tare da duk mai tausaya ma game da halin kunci da yaki da s**a kewaye mu mutanen arewa! da fatan zakuci gaba da taimaka mana da addu'a

07/11/2018

a irin wadannan kwanaki ne muke bukin murnan haifuwa shehu mujaddadi Dan fodiye.

06/10/2018

Duk wani mumunan abu akasan nan yana karewa ne akan musulmi dan arewa

20/07/2018

TARIHIN SHEIKH USMAN DAN FODIYO (R.A) A CIKIN TAMBAYA DA AMSA.
KASHI NA 1.

ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ.

TAMBAYA: Ya sunan Mahaifin Shehu dan Fodiyo?
AMSA: Muhammadu Fodiyo (r.a).

TAMBAYA: Ya sunan mahaifiyar Shehu danFodiyo?

AMSA: Hauwa'u 'yar Muhammad dan Usman.

TAMBAYA: A wacce shekara ce aka haifi dan Fodiyo (r.a)?

AMSA: An haifi Sheikhu dan Fodiyo ne a shekara ta 1169 bayan hijra, wanda yayi daidai da 1754 miladiyya. Kusan shekaru 300 da s**a shude kenan.

TAMBAYA: A wanne gari ne aka haifi dan Fodiyo (r.a)?

AMSA: An hafi Shehu ne a garin DAGEL ta cikin daular Gobir.

TAMBYA: A ina Shehu ya fara karatunsa na addini?.

AMSA: Lallai Shehu ya yi kusan kaso 85 bisa dari na karatunsa ne a Gida, kana daga kan Mahaifinsa da Kakkanninsa da 'yan uwan Mahaifinsa.

TAMBAYA Ko za mu ji sunayen Malaman da ya yi karatu a hannunsu?

AMSA: Ga wasu daga cikin malanan Shehu (r.a) :

1. Muhammadu Fodiyo mahaifinsa. Ya yi karatun Alkur'ani ne a wajen sa

2. Mahafiyarsa Hauwa'u (r.a).

3. Kakarsa mai suna Rukayya 'yar Muhammad dan Sa'ad.

4. Sheihkh Usman wanda aka fi sani da BABDU AL-KABAWIY. A wajen sa Shehu ya karanci Littafin ISHRINIYA da mak**antan ta.

5. Sheikh Abdurrahman dan Hammada. Shehu ya karanci Ilmin Nahwu a wajen sa. Kamar littafin Alfiyyar dan Maliku da sauran su.

6. As-Sheikhul Allama abul amana JIBRIL BN AMR. Shehu ya shekara cur yana karatu a wajen sa, kuma a wajen sa ne Shekhu ya yi mafi yawan karatuttukansa k**ar: TAFSIRI, FIKHU, HADISI da sauran su.

7. Kawunsa As-Seikh Alhaj Muhammad Raji bn Mu'addab.

8. As-Sheikh Allama Hashim Zamfary.

TAMBA: Ko za mu san Sunayen 'yayan Shehu dan Fodiyo (r.a)

AMSA: Shehu yana da 'ya'ya k**ar haka:

1. Muhammadu Sa'adu. Shi ne babban dan shehu.
2. Muhammad Sambo.
3. Muhammadu Bello.
4. Abdul kadir.
5. Ali As-shazaly.
6. Abubakar.
7. Muhammadu Bukhary.
8. Umar.
9. Muhammad Hajo.
10. Hasan.
11. Asma'u
12. Khadija.
Dukan su su 12 manyan malamai ne da kowannen su Jami'ar kansa ne mazan su da matan su.
Litattafan da aka duba:
ﺍﻟﻤﺮﺍﺟﻊ1 ﺇﻧﻔﺎﻕ ﺍﻟﻤﻴﺴﻮﺭ ﻓﻲ ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺑﻼﺩ ﺍﻟﺘﻜﺮﻭﺭ، ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻠﻠﻮ ﺑﻦ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﺑﻦ ﻓﻮﺩﻱ .2 ﺗﺰﻳﻴﻦ ﺍﻟﻮﺭﻗﺎﺕ ﻟﺒﻌﺾ ﻣﺎ ﻟﻲ ﻣﻦ ﺍﻷﺑﻴﺎﺕ، ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻓﻮﺩﻱ .3 ﺇﻳﺪﺍﻉ ﺍﻟﻨﺴﻮﺥ ﻣﻦ ﺃﺧﺬﺕ ﻋﻨﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻴﻮﺥ، ﻻﻟﺸﻴﺦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻓﻮﺩﻳﻠﺸﻴﺦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻓﻮﺩﻱ .4 ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻓﻲ ﻧﻴﺠﻴﺮﻳﺎ، ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺁﺩﻡ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻹﻟﻮﺭﻱ .5 ﺍﻟﺜﻘﺎﻓﺔ ﺍﻟﻌﺮﺑﻴﺔ ﻓﻲ ﻧﻴﺠﻴﺮﻳﺎ، ﻟﻠﺪﻛﺘﻮﺭ ﻋﻠﻲ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮ .
Akwai ci gaba in sha'Allah.

Haduwata da Pasto Yuhana D.Y Buru a Arewa House Kaduna.Tunanina ya canja gameda mutanen dake mulkin Najeriya. Haka tunan...
25/06/2018

Haduwata da Pasto Yuhana D.Y Buru a Arewa House Kaduna.
Tunanina ya canja gameda mutanen dake mulkin Najeriya. Haka tunani ya canja kan wasu gungun tsofafi
da ake kira Dattijan Arewa.(A.C.F)
Mafi ban haushi A.C.F wadanda nayi alkawali duk salar farilla sai na roki Allah ya tsinewa wadannan
gungun tsofafin Azzalumai da Duniya ta cutu da shairinsu tun sunada karfi.
Dalilina shine wadannan mutane da saninsu ake Dora ko wane shugaba a Kasar nan. Haka suna sane da
duk wata kutingwila da akewa Arewa. Mafi akasarinsu tsofafin Janarori ne ,Shugabani,Ma'akata Sarakuna
da sauran su.
Rashin adalcin su yasa Arewa ta koma filin Yaki yau nan gone can
Boko Harama a Jahohin BORNO,YOBE,ADAMAWA da Sauransu Arewa maso gabas
FULANI da MANOMA
Binuwai, Nasarawa da Taraba
SATAR MUTANE DA GARKUWA DASU
Kaduna,Abuja da Birnin Gwari.
BARAYIN SHANU DA KISAN KARE DANGI
Zamfara da Katsina
Duk wannan musifar an hadasata ne domin Arzikin dake kwance Arewa cin Najeriya Wanda ake son kwasa
akai kasashen Turai.
Zinare dake Dajin Birnin Gwari zuwa Zamfara Wanda masana arzikin karkashin kasa s**a tabbatar cewa
zai ishi duk kan Afirika Ba Najeriya Ka dai Ba.
Maiduguri zuwa Sakkwato fetur me shinfide mai KYAU Wanda Duniya ke bukata yanzu.
Binuwai, Taraba ,Nasarawa
Arziki na nan kasa shimfide
Wadan nan Dalililai sune makasudin yakar Arewa.
Kamar yadda suke yakar kasahen Afirika masu arziki iron Somaliya Sudan Libiya da sairansu
Duk wadan nan take yaken Turawan yamma ne ke kwasar Arziki kuma da sanin Shugabanin kasar nan da
Dattawan Arewa.
12/12/2015 da rana tsaka Sojoji s**a dinga kisan Yan shi"a zar zuwa 14/12/2015 akace sun tare hanya
ne ga Shugaban Rundunar Soja Lt.janar Tukur Yusuf Burutai Ashe karya CE shiri ne tsarare na tarwatsa
Arewa.
Kwana daya da afkawa Yan Shi'a sai ma'abuta HANKALI s**a fara bincike saboda a tarihin Najeriya ba'a
taba kisan kiyashi Ba na wasu jama'a Yan kasa mafi muni da keta Hakken Bil'adam k**ar na Zaria.
KALAMAI MASU KARO DA JUNA.
Suntare hanya...RUNDUNR SOJA
Sunyi kwanto Bauna...B.b.c Hausa ,V.O.A Hausa e.t.c
Sunyi Gwamnati Cikin Gwamnati...Janar Buhari
Basu bin doka...Gwamna el'Rufa'
Iran ke turumusu kudi ita suke bi tana basu mak**ai...Malaman Izala,Da wasu bangarori na musulmi.
Yaku ma"abota adalci da son gaskiya kuyi nazarin wadannan kalamai.
Miyasa aka afkawa Zakzaky ?
Amsar it a CE
Shikadai ne Malamin da Baya tareda gwamnati haka shika dai ne ya rage Arewa Wanda baya tsoron
gwamnati shakadine ne ke iya fadar komi shika dai ne mai mabiya matasa wadanda zasu iya kawo sauyi
a wannan kasar watarna
Kusa HANKALI kuyi tunani Ku zamo adillai kuyi adalci ga kowa koda makiyinku be.

Address

Dakwa

Telephone

+2348078489947

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Daulan Shehu Dan Fodiyyo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Daulan Shehu Dan Fodiyyo:

Share