It's Badaru s wapa

It's Badaru s wapa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from It's Badaru s wapa, Business service, Kano, Dal.

07/10/2024

HARYANZU BAKA DAINA TUNANIN CEWA MAN FETUR ZAI DAWO ₦240 ? TO YA KAMATA KA FARKA DOMIN MAFARKI KAKEYI.

Mazaje ku saurare ni dakyau. Matukar kana ɗaya daga cikin masu tunanin cewa wai FETUR zai dawo ₦240 duk lita ɗaya to ka tanadi gadonka a asibitin ciwon zuciya da hawan jini. Dole ne ka yarda cewa hasashenka bashida tabbas sannan kuma bazai taɓa yiyuwa ba . Duk wanda yace maka FETUR zai dawo ₦240 to ya raina tunaninka ne dakuma iliiminka.

Mazaje wannan fa ba abun yiwa ƙorafi bane ba . Domin ƙorafi ɗabi'ar ragon namiji ce kasalalle. Kaikuwa jarumi ne. Menene abunda yakamata Kayi? Shine ka faɗaɗa hanyar samun kuɗinka sannan kuma kadaina dogara da albashinka.

Dolene idan kanaso ka tsira daga wannan matsananciyar rayuwar da take shaƙe mutum ta WUYA , to saika canja zubin tunanin ka akan kuɗi, sai ka daina baƙin tunani irin na talaka , kadawo tunani irin na masu kuɗi. Kanaso rayuwa tayi maka sauki? To ka tunkareta.

Fara yin kasuwanci yanzu sam-sam ba zaɓi bane ba, dolene idan kanaso ka tsira daga wannan ƙunci da tsananin saika fara kasuwancin da kake samun kudi ta gefe guda. Kasuwancin da kake da iko akan sarrafa farashinshi . A tunaninka wadanda suke da iko akan ƙara farashin kayansu idan FETUR ya kara kudi suna shan wannan wahalar? Ka sake tunani.

Yayinda FETUR ya ƙara kuɗi, to suma zasu ƙara farashi. Idan yaƙara ƙara kuɗi to suma zasu ƙara ƙara farashi. To aciki wanene yake shan wahala? Kaima kasani. Wahalar da ake sha ta shafi mamallakan business din ? Sam sam. Kai ne dai wanda ya zauna yana ƙorafe-ƙorafe acikin wahala . Kuma kaine wanda yake azabtuwa idan FETUR ya kara kuɗi. To akan me bazaka yi yunkurin canja zubin rayuwarka ba?

Ka fara kasuwanci.
Ka mallaki kanka.
Ka tsallake wannan tsananin.
Babu wanda zaiyi maka hakan sai kai.
Akwai abubuwa dayawa a gabanka.
Ka rayu cikin aminci.

Follow Ibrahim reco kano

Address

Kano
Dal

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when It's Badaru s wapa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share