Real Muhammad Alh bukar

Real Muhammad Alh bukar Always thank God 🙏

04/05/2023

Gwabzawar Wike Da Tinubu Darasi ne ga Ƴan Siyasar Arewa

Ya k**ata abinda ya faru jiya tsakanin Shugaban Ƙasa Mai Jiran-Gado Bola Tinubu da Gwamnan Ribas Nyelsom Wike ya zama darasi ga ƴan siyasar Arewa.

A daidai lokacin da gwamnonin Arewa masu barin gano ke ta kamun ƙafa domin su samu muƙamai a sabuwar gwamnati, abinda ya damu Wike shine jiharsa ta zama ta farko da Tinubu zai ziyarta bayan cin zaɓe. Ko da Tinubu ya isa jihar Ribas, ashe Wike yana da ajanda. Maimakon ya nemi wani abu na buƙatar kansa, sai ya nemi abinda zai amfani jiharsa. Ya roƙi cewa idan Tinubu ya k**a mulki, yana so Tinubun ya dawowa da Ribas kuɗaɗen hanyoyin da ya gina waɗanda Tinubun ya bude. Wike ya ce tun hanyoyin na tarayya ne, k**ata yayi Gwamnatin Tinubu ta mayar wa Ribas kuɗin da ta kashe. Kada fa mu manta cewa Wike ba shine gwamnan Ribas a lokacin da za a dawo da ƙudin da ya nema a biya. Akwai darasi anan.

Sannan akwai darasi akan yadda Tinubu ya bawa Wike amsa. Da yake Tinubun gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya san abinda yake, sai ya ƙi wayon. Take yanke ya maida wa Wike amsa da cewa "A'a, ba kwa bina ko sisi. Dama hanyoyinku ne, ku kuke amfani su kuma kun gyara su. Saboda haka, mun yaba muku". Da wani baƙauyen ɗan siyasan ne da tulin jama'a da ƙasar aka tara masa, sun yayi gwaninta tun kafin ya amshi mulki. Da tuni ya amsa buƙatar Wike yayi alƙawarin cewa zai dawo wa da Ribas kuɗin da aka kashe akan hanyoyin.

Wike bai samu abinda ya nema ba amma ya nuna cewa jihar ce a gabansa. Yana da wuya ayi Gwamnatin Tinubu ba tare da amma wa Wike muƙami amma wannan bai hana shi sanya buƙatar jiharsa gaba ba. Amsar Tinubu kuma ta nuna cewa wayeyyen ɗan siyasa baya yarda a tara masa ƙasa a kife shi. Wannan ma babban darasi ga ƴan siyasan da ake kira a basu mulkin gargajiya a wata uwa duniya domin a karɓe ƴan sulenlan al-umma da aka ba su amana.

Address

Damaturu

Telephone

+2347010171313

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Real Muhammad Alh bukar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Real Muhammad Alh bukar:

Share