07/02/2026
TIRKASHI: Daga ranar da na ci mulki, tun kafin na shiga ofis, zan dakatar da Mauludi a faɗin Jihar Gombe — Sheikh Professor Isa Ali Pantami
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa su malamai ne na Ahlus Sunnah da ke da cikakken ƙudurin yaƙi da bidi’a a duk inda ta bayyana.
Pantami ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya yi, inda ya ce sun ɗauki alƙawari a tsakaninsu cewa duk ranar da Allah Ya ba su nasara kan duk wani muƙami da suke nema, to ƙarshen duk wani nau’in bidi’a ya zo ƙarshe.
“Mu malamai ne na Sunnah da muke yaƙi da bidi’a. Na yi alƙawari cewa duk ranar da Allah Ya sa muka samu nasara kan muƙamin da muke nema, lallai ƙarshen dukkan wani bidi’a ya zo ƙarshe, domin ba za mu bari ana saɓawa wa Allah ba,” in ji Pantami.
Jawabin Farfesa Pantami ya jawo muhawara a tsakanin al’umma, musamman a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin kalaman a matsayin kira ga tsaftace addini, yayin da wasu kuma ke nuna damuwa kan yadda hakan zai shafi zaman lafiya da fahimtar juna a cikin al’umma.