Salisu jos

Salisu jos Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Salisu jos, Business service, Asibitin Central, Funtua.

Tattaunawar sulhu da barayin daji a irin wannan yanayi na rashin tsaro babban mataki ne, amma kuma yana bukatar taka-tsa...
06/03/2026

Tattaunawar sulhu da barayin daji a irin wannan yanayi na rashin tsaro babban mataki ne, amma kuma yana bukatar taka-tsantsan don gudun kada a ba wa miyagu damar sake karfafa kansu. Ga yadda za a iya bin tsarin sulhu mai dorewa:
1. Tantance Masu Son Sulhu na Gaskiya
Ba kowane dan bindiga ne yake son sulhu don zaman lafiya ba; wasu suna yi ne don su huta ko su sake samun mak**ai.
Rarrabe Tsakaninsu: Dole a raba tsakanin wadanda s**a shiga harkar saboda zalunci ko rashin ilimi, da kuma wadanda s**a mayar da abun sana’ar neman kudi.
Tabbatar da Shugabanci: Dole ne a tabbatar da cewa wanda ake sulhu da shi yana da iko a kan yaransa, domin kada a yi yarjejeniya da shugaba amma yaran su ci gaba da kai hari.
2. Sharuddan "Mika Wuya" (Disarmament & Reintegration)
Sulhu ba kawai a daina harbi ba ne; dole ne a bi matakai na musamman:
Mika Mak**ai: Sharadi na farko dole ne ya kasance mika dukkan mak**an da ke hannunsu ga hukuma.
Tantance Su: Gwamnati ta dauki bayanansu (biometrics) domin idan s**a koma gidan jiya, a san su da sauri.
Sake Gyara Halayya: Ba su horo na addini, tarbiya, da sana’o’i don su zama mutane nagari a cikin al'umma.
3. Sanya Masu Ruwa da Tsaki (Inclusivity)
Sulhun da aka yi a ofishin gwamnati kawai ba ya dorewa. Dole ne a hada da:
Wadanda aka Zalunta: Idan har wadanda aka kashe wa dangi ko aka kwace wa shanu ba su yafe ba, sulhun ba zai dade ba. Dole a biya diyya ko a samar da hanyar warkar da radadin zuciyarsu.
Malamai da Sarakuna: Su ne za su zama kashin bayan yarjejeniyar ta fuskar rantsuwa da tabbatar da gaskiya.
4. Adalci ga Kowa (Justice and Equity)
Sulhu ba yana nufin a bar mai laifi ya tafi haka kawai ba.
Hukunci ga Manyan Masu Laifi: Wadanda s**a aikata manyan laifuka na kisan kiyashi dole su fuskanci shari'a ta musamman.
Hana Kyamar Wadanda S**a Dawo: Dole ne a koya wa al'umma yadda za su karbi wadanda s**a tuba da gaske ba tare da kyamata ba, don kada hakan ya sa su sake komawa daji.
Misalin Kasashen da S**a Yi Nasara
Kamar yadda aka gani a kasashen irin su Rwanda ko kuma tsarin Amnesty na yankin Delta a Najeriya, nasarar tana nan ne idan har aka mayar da hankali kan ci gaban yankin da kuma samar da ayyukan yi.
Gargadi: Sulhun da aka yi ta hanyar ba wa ‘yan bindiga kudi kawai yana kara ruruta wutar ne, domin suna amfani da kudin wajen siyan karin mak**ai. Dole sulhun ya ginu kan "Zaman Lafiya don Ci Gaba" ba wai "Kudi don Zaman Lafiya" ba... zanci gaba..
Salisu lawal jos

"Irin wadannan bayin Allahn basu ɗauki mutuwa a matsayin ƙaskanci ba, koda yaushe idan tazo suna maraba domin sun tafiya...
28/02/2026

"Irin wadannan bayin Allahn basu ɗauki mutuwa a matsayin ƙaskanci ba, koda yaushe idan tazo suna maraba domin sun tafiya ne akan tsarin da baya rushewa saboda faduwar wani Jagora.

Duk wanda yake tsoron mutuwa ba zai shiga yaƙi da Amurka ba idan yaso sai ya miƙa wuya k**ar yadda sauran Munafukan Shugabanni s**a zama karnukan farauta.

Muna addu'ar Allah yaci gaba da bashi kariya a duk inda yake ya rusa tanadin makiyan cikin gida da na waje... Sunusi

Aisha Muhammad Dan Allah GA sako aba mai girma gommna [25/2/2026]​Zuwa ga:Mai Girma Gwamnan Jihar Filato Jos His Excelle...
25/02/2026

Aisha Muhammad Dan Allah GA sako aba mai girma gommna
[25/2/2026]
​Zuwa ga:
Mai Girma Gwamnan Jihar Filato Jos
His Excellency: mutfwang:
​Kira na Gaggawa kan Daukar Matakan Tsaro don Kare Rayukan Matafiya a Hanyoyin Jihar Filato
​Mai Girma Gwamna,
​Ina rubuta wannan wasika ne a matsayina na dan kasa mai kishin jihar mu, domin mika koke da shawarwari kan yawaitar hare-hare da kisan gilla da bata-gari ke yi wa matafiya da mazauna garin Jos a kan manyan hanyoyinmu. Wadannan abubuwa na bakin ciki suna barazana ga zaman lafiya, tattalin arziki, da hadin kan jihar mu.
​Domin samun maslaha mai dorewa, ina ba da shawarar matakai k**ar haka:

​Share Kurmi da Gyaran Hanyoyi: Muna kira ga gwamnati da ta sa a sassabe daji da ya mamaye gefen hanyoyi, sannan a gyara ramukan da ke sa motoci rage gudu, wadanda ke zama tarkon kisa.
​Karfafa Operation Rainbow: Muna bukatar ganin jami’an tsaron jihar sun kara kaimi tare da ba su kayan aiki na zamani don yin sintiri a kananan hanyoyi.
​Hukunta Masu Laifi: Muna rokon gwamnati ta tabbatar an hukunta duk wanda aka k**a da hannu a wadannan ayyukan ta’addanci a gaban idon jama’a don ya zama darasi ga wasu.
​Mai Girma Gwamna, muna da yakinin cewa idan aka dauki wadannan matakai, Jos za ta sake zama cibiyar zaman lafiya da yawon bude ido k**ar yadda aka san ta.
​Muna fatan za a duba wannan koke cikin gaggawa.
​Nagode.
​Naka mai biyayya,
Salisu lawal jos

Inganta zaman lafiya a cikin al'umma mai mabambantan addinai da kabilu k**ar Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, amma abu n...
25/02/2026

Inganta zaman lafiya a cikin al'umma mai mabambantan addinai da kabilu k**ar Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, amma abu ne mai yiwuwa idan kowa ya sa hannu. Zaman lafiya ba kawai rashin faɗa ba ne; yanayi ne da kowa yake jin ana damawa da shi kuma yana samun adalci.
​Ga wasu muhimman hanyoyi da za a iya bi domin inganta zaman lafiya:
​1. Ilimantarwa da Wayar da Kai
​Yawancin rikice-rikice suna faruwa ne saboda rashin sani ko kuma mummunar fahimta game da addinin wani.
​Fahimtar Juna: Ya k**ata a koya wa matasa darasin zaman tare a makarantu da masallatai da coci-coci.
​Hadin Gwiwa: Malamai da fastoci su rinka zama tare domin nuna wa mabiyansu cewa zaman lafiya shi ne asalin koyarwar addini.
​2. Adalci da Daidaito
​Inda babu adalci, zaman lafiya yakan yi wuyar samu.
​Gaskiya a Shari'a: Ya k**ata hukuma ta rinka hukunta duk wanda ya tada rikici ba tare da duba addininsa ko matsayinsa ba.
​Rarraba Arziƙi: Rashin ayyukan yi da fatara na sa matasa shiga rigingimu cikin sauƙi. Idan aka samar da ayyukan yi, mutane za su fi mayar da hankali kan neman abinci.

25/02/2026

It is important for the authorities in Plateau to come out and do what is necessary... as soon as possible.

06/02/2026
وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلِهِ الرُّسُلُ أَفَإِنْ مَاتَ أَوْ قُتِلَ انْقَلَبْتُمْ عَلَى أَعْقَ...
27/11/2025

وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلِهِ الرُّسُلُ أَفَإِنْ مَاتَ أَوْ قُتِلَ انْقَلَبْتُمْ عَلَى أَعْقَابِكُمْ وَمَنْ يَنْقَلِبْ عَلَى عَقِبَيْهِ فَلَنْ يَضُرَّ اللَّهَ شَيْئًا وَسَيَجْزِي اللَّهُ الشَّاكِرِينَ

Mai kake tunani da  kasar data Tara irin wa'innan mutanan...1-MALAMAI..MA KWADAITA2-SHUWAGABANNI.AZZALUMAI3-SAURAN.MABIY...
22/11/2025

Mai kake tunani da kasar data Tara irin wa'innan mutanan...
1-MALAMAI..MA KWADAITA
2-SHUWAGABANNI.AZZALUMAI
3-SAURAN.MABIYA.(TALAKAWA).WAWAYE,??

GA WATAN MAULIDI YA SHIGO.Waɗannan su ne Nasihohina ga ƴan maulidi.1- Mu guji karanta tatsuniyoyin ƙarya wurin taron Mau...
24/08/2025

GA WATAN MAULIDI YA SHIGO.
Waɗannan su ne Nasihohina ga ƴan maulidi.

1- Mu guji karanta tatsuniyoyin ƙarya wurin taron Maulidai.

2- Mu guji ƙirƙirar falalolin ƙarya muna jinginama shugaban halitta S A w, Annabi ya wadatu daga duk wata daraja ta ƙarya.

3- Mu tsaya inda Shari'a ta tsayar damu, ka da mu wuce makaɗi da rawa.

4- Mu guji cakuɗar maza da mata wurin taron Maulidai, ba le maza da mata su haɗe wuri ɗaya ana cashewa da raye-raye.

5- Mu guji shagaltuwa wurin kawo hujjar yin taron maulidi.

6- Mu shagaltu da karanta tsaftatatciyar sirar shugaba S A W sahihiya dake cike da Insaniyya.

7- Mu yi ƙoƙarin nusar da al'umma cewa : wanda baya Maulidi ba maƙiyin Annabi S a w bane, kuma rashin yin taron maulidi ba shine ke nuna wanda baiyi taron Maulidin ba baya murna da haihuwar Annabin Rahama s a w ba.

8- Mu guji Kiran waɗanda basu Maulidi da kalmomi, k**ar "Maƙiyaa Annabi" Ko siffantasu da rashin son Annabin Rahma S.a.w.

9- Mu yi ƙoƙari matuƙa wurin zaburar da Al-ummarmu akan massala ɗabi'un Girma kyawawa, da aka aikosa domin cikasu, k**ar Gaskiya, riqon amana, adalci, cika alƙawali da sauransu, Saboda waɗannan halayen ne Annabi S A W yace " An Aiko ni domin in cika Ɗabi'u/ Halaye/ Tadodin Girma.

10- Mu yi maulidi, don neman yardar Allah da neman kusanci ga masoyinsa, wannan shine kyautata niya.

10- Ka da muyi maulidi don ɓata rayuwar waɗanda ba su yin maulidi ko cin Zarafinsu ko huce haushi akansu.

11- Mu kiyaye haƙƙin maƙwabta ta hamyar sassauta sautin lasifukunmu cikin dare, a halin waƙe-waƙen da mu keyi na bege da karatu, ka da Shaiɗan ya ruɗeka da cewa : ai Yabon Annabi ne ko faɗar falalarsa ake faɗa, ka sani ko Karatun Alqur'ani mai girma, ba a yarda sautin karatunsa da kake yi ya hana wani Mutum baccinsa ba, ba le kayi masa tilas ɗin dole sai ya saurareka.

12- Ka da mu fake da Guzuma mu harbi karsana, wannan yana nufin ka da mu kira Mutane da sunan gaya musu "Falalolin Annabinsu da kyawawan halayensa", daga ƙarshe mu koma karantar da "Karamomin@ami

Kasa tatara gurbatattu lauyoyi,da alkalai ,da malamai,tayaya shuwagabanni bazasuke mulki irin na dabbobi ba,
01/11/2024

Kasa tatara gurbatattu lauyoyi,da alkalai ,da malamai,tayaya shuwagabanni bazasuke mulki irin na dabbobi ba,

25/10/2024

Shima fa rashin wutar nan a arewa zunubanmu s**a ja mana ko?🤔

14/10/2024

With Comr Abba Sani Pantami – I just got recognized as one of their top fans!

Address

Asibitin Central
Funtua

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Salisu jos posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share