Sheikh Mas'ud Hashim Kurmi

Sheikh Mas'ud Hashim Kurmi Mun bude wannan page ne domin yada sunnar Annabi s.a.w

27/08/2022
21/04/2022
23/01/2022

Kamar yanda page dinnan ya koma haka🖕haka shima profile zai koma😎🙇🙇🙇

Ya Baye💖💖💖💪💪💪
23/01/2022

Ya Baye💖💖💖💪💪💪

20/08/2021

YAZIDU AGUN SHEIKH AHMAD TIJJANI R.T.A !!

Zalunci Mafi Muni Shine Zaluncin da Yazidu yayi na kashe Jikokin Annabi S.A.W akan haƙƙin su.

Shine ya saka aka kashe Sayyadina Hassan, kuma ya saka aka kashe Sayyadina Hussain ƙaninsa, Wannan ba ƙaramin Zalunci bane ba.

Shiyasa mu Tijjanawa Muna tsinewa Yazidu Kamar Yadda Maulanmu Shehu Tijjani ya tsine mai a cikin Littafin

الإرشادات الربانية بالفتوحات الإلـٰهية

Sharhin da Shehu Yayi wa Hamziyya ta Imamul Busiri, Gun da yazo kan Ƙadiyyar da shi Busiri ke nuna ɓacin ransa da damuwa da Abubuwan da akayi na kisan gilla ga Jikokin Annabi S.A.W agun da yake fassara baitin:

من شهيدين ليس ينسيني الطفْٰ
فُ مصابيهما ولا كربلاء

Shehu Radiyallahu Anhu yace:

من شهيدين ليس ينسيني، أشار بهذا البيت إلى أنهما مقتولان معا

Wannan bitin yana nuni da cewa Dukkan su su Biyun Kashe su akayi.

أما الحسن فقتله يزيد بن معاوية، وذلك أنه بعث إلى زوجته إن سقته سما قاتلا أعطاها مائة ألف فسقته وعليه لعنة الله فهذا هو الشهيد أول.

Amma Sayyadina Hussain R.T.A Yazidu Ɗan Mu'awiyah ne ya kashe shi, ta hanyar turawa matar sa da Sanar da ita cewa, da zarar ta shayar dashi Sammu me kisa toh ze Bata dinare duba ɗari, ta kuma shayar dashi, Shehu Tijjani yace: Allah ya tsine masa. Wannan shine Shahidi na Farko.

والشهيد الثاني الحسين قتل بالطف من كربلاء وهو مكان مشهور من ناحية العراق، وهناك قتل في خمس مائة رضي الله عنه، فيهم ثلاثة وثمانون من بني هاشم ومنهم سبعة عشر من أولاد علي رضي الله عنه.

Yace: Shahidi na Biya Shine Sayyadina Hussaini wanda aka kashe a Ilɗuf a Karbala, guri ne Mashhuri a Nahiyar Iraƙ, acan aka kashe shi a cikin mutum Ɗari biyar, a cikinsu Akwai mutum 83 daga Banu Hashim Akwai kuma mutum 17 daga yaran Sayyadina Aliyu R.T.A.

Shehu a ƙarshen bayaninsa na wannan baitin ya ƙare tsinewa Yazidu da wanda ya saka ya kashe shi الشمر بن ذي الجوشن.

Kuma daman tsinannu ne da nassir Ƙur'ani Saboda sun cutar da Annabi S.A.W .

Allah kuwa ya faɗa cikin Cutar da Annabi a Alƙur'ani:

إن الذين يؤذون الله وروسوله لعنهم الله في الدنيا والآخرو وأعد لهم عذابا مهينا.

Wanda s**a cutar da Allah da Annabinsa S.A.W Allah ya tsine musu a Duniya da lahira kuma ya tanadar musu Azabar Wulaƙanci.

Banjin Akwai cutar wa kamar a Kashewa Annabi S.A.W Jikoki Guda Biyu ya'yan 'yarsa da yafi so tsokar sa.

A ƙarshe ina faɗa kamar yadda Busiri ya faɗa:

كل يوم وكل أرض لكربي
منهم كربلا وعاشوراء

Kowace Rana da Kowane Guri ga Bakin ciki na na wannan kisan Gillar, Karbala ne da Ranar Ashura.

Wannan ita ce Matsayar Maulanmu kan wannan Ƙadiyyar kuma muma akanta muke.

amma Maganar Sahabbai da Abunda ya gudana tsakanin su wannan ba ruwan mu bazamu saka baki kamar yadda shima be saka baki ba zamu tsaya kan:

والإمساك أو الكف عما شجر بين الصحابة

Shima Yazidu ba Sahabi bane domin bega Annabi S.A.W ba kamar yadda Malaman Tarihi S**a tabbatar.

Allah ya jaddada tsinuwar sa ga Wanda s**ayi wannan Kisan Gillar, ya kuma ƙara yarda ga shahidai Guda Biyu da aka kashe da Mahaifinsu da Mahaifiyar su da dukkan Sahabban Annabi S.A.W.

Shareef Ahmad Mukaddam

09/08/2021

TARIHIN KHADIMUL QUR'AN KHALIFA SHEIKH ISHAQ RABI'U DA GUDUNMUWAR GA ADDINI

An haifeshi a gidan Sheikh Muhd Rabi'u Dan Tinki, daya daga Many an Malaman addini a Arewacin Nigeria, ya Shahara da Qur'ani da Ilmi Sheikh Nasiru Kabara Kano na cikin Almajirans

Tun daga Mahaifinsa har Kakansa na 5, duka Gwanayen Qur'an ne Mahaddata, yayi Haddar Qur'ani wajen Mahaifinsa 1936_1942 ya Kuma koyi Larabci da sauran ilmoma

Ya tafi Maiduguri domin kara Karatu, yadawo gida yayi Auren farin, ya sake Komawa Zaria a gidan Mal. Na'iya ya kara karatu Shekaru 2 yazama Malami she karat 1949 yafara koyarwa

Ya fara karanta da Qur'ani da Larabci da Ilmi, da Shekaru 24, a farkon 1950, yafara Kasuwanci da Shekaru 25, koda yake bai daina Karantarwa ba, ya kafa Kamfani 1952 Ishaq Rabiu & Sons

Ya fara da zama dilan UAC na kekunan dinki da littafan addini, a 1958 Kamfabin ya bunkasa, da aka kafa Kaduna Textile yazama babban dila ya zama babban dilan Kamfanin Arewacin Nigeria

Kuma shi da wasu 1963, s**a kafa Kano Marchent Trading Company, ya Kuma kafa Kamfanin Dunka kayan sawa, 1970 ya goyi bayan NPN a Jamhriya 2, ta kafa Gwamnati

A 1972, ya kafa Bagauda Textile ya Kuma kafa wasu kananan kamfuna don taimakon mutane da bunkasa tattallin arzikin Kasa yayi Wafati da Shekaru 93 a shekarar 2018, yabar mata 4 da 'ya'ya 63 da Jikoki masu matukar yawa sosai

SHAHARARSA A NIGERIA DA DUNIYA

Ya Shahara ne da Qur'ani da Khudimarsa kuma ya Shahara a Kasuwanci da Taimakon Jama'a .

Ya kwashe Fiyeda Shekaru 70, Qur'ani na cikin Kansa yana karantashi dare da rana yana bada Sallar Tahajjud dashi yana Khidimar Quran da Makarantarsa da Mahaddata tsawon rayuwarsa

Har ya Gina Jami'ar Qur'an shi kadai, Gadon Maya, ya Gina Masallatan Sallolin Farilla dana Juma'a a wurare da yawa daga cikinsu akwai:

1. Sheikh Muhd Rabi'u Goron Dutse 1983
2. Sheikh Ahmad Tijjani Kofar Mata 1996
3. Sheikh Ibrahim Inyass Gadon Kaya 2008
4. Sheikh Ishaq Rabiu Jakara 2015
5. Sheikh Sharif bn Salim Kwankwasiyya 2019
6. Jami'ur Rasul Kwarin baka Sabuwar Gwandu

Ya Gina Gidaje 60, ya baiwa Mahaddata Wakafi
Ya Tatar da Library ta Mahaifinsa ta littafai fiye da 2000, ya maida fiyeda 5000, ya samu lambobi na yabo a kasa da duniya da yawa

Ya Shuganci Kungiyoyin Addini a Nigeria da wajenta fiyeda 10, bayan Zamowarsa Khalifan Tijjaniya a Nigeria, kuma Shugan Majalisar ta na Shura

Member ne a Majalisar kula da Masallatai ta Duniya, Member ne a Majalisar tsara aiyukan cigaban Musulunci ta duniya, dake Makka, kuma Jagora ne a Munazzamatu Fityanil Islam

Allah ya fada a Qur'an, Wadanda suke karanta Littafin Allah s**a tsaida Sallah s**a ciyar daga abinda muka arzurtasu bayyane da 6oye suna kwadayin Kasuwanci (da Allah) da babu hasara ( Khalifa yayi wannan da aka fada)

Har Allah yace sai muka gadar da Littafin (Qur'an) ga wadanda muka za6a daga bayinMu ya shiga cikin Za6a66u Fadir 32

A Hadisan Falalar Mahaddata Annabi saw yace

Masu Qur'ani sune Mutanen Allah Ibn Majah
Mafi Alherinku Wanda ya koyi Qur'ani ya koyar (Bukhari, Muslim, Tirmiziy, Nasa'i Abu Daud )

Allah ya daga darajar wasu mutane da Quran, Muslim ( Kamar dai shi Khalifa)

TA FUSKAR TAIMAKON JAMA'A Annabi yace:

Mafi Alherin Mutane Wanda rayuwarsa tayi tsawo aikinsa yayi kyau Tirmiziy
Wanda yasamu damar taimakon Dan Uwansa to ya taimakeshi Muslim
Idan Adam ya mutum aikinsa ya tsaya sai dai Abu 3, duk ya samesu, 1, Sadaka mai gudana, 2, Da mai masa Addu'a, 3, Ilmi daya koyar

Abubuwan da yawa kamar Daukar nauyin Dalibai suyi karatu a Jami'o'in Madina, Sudan, Niger, Nigeria da sauran su Kula da Marayu, Marasa lafiya, 'Yan gidan Yari, Gajiyayyu, Tsoffi

Allah Ina rokonKa da Sunayenka da Siffofinka ka Kara Gafara da RahmarSa da kusanci da yarda ga Khalifa Ishaq Rabiu Khadimul Qurani
don Girman Annabi saww da Qurani

Ya Razzaku, Ya Wahhabu Ya Mu'udi, Ya Barru Ya Kareemu Kai mana baiwar irin Arzikinsa da irin Aiyukansa na Alheri don mu rabauta muma.

Annabi saww yayi Gaskiya Madallah da Duniya ta kwarai ga Mutumin Kirki, kamar dai Maulana Sheikh KHALIFA Ishaq Khadimul Qur'an RTA.

Abdulhakeem Ahmad Ya'akub Gusau

Address

Garki Ii

Telephone

+2347035225731

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Mas'ud Hashim Kurmi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share