26/09/2023
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
KUNJI MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM
Bayan an kammala yaqin Hunainu, yayin da Manzon Allah (S.A.W) yazo rabon kayan ganimah, sai ya rarrabata atsakanin mutanen Makkah da sauran Qabilun larabawa wadanda basu dade da shiga musulunci ba.
Mutanen Madeenah kuwa (AL ANSAR) bai basu komai ba. don haka sai wasu daga cikinsu suke mamakin mai yasa Manzon Allah (S.A.W) bai raba ganima dasu ba? Alhali tare dasu akayi gwagwarmayar nan!!
Da maganar tazo kunnensa (S.A.W) sai ya tarasu gaba dayansu waje guda yayi musu jawabi mai ratsa zukata, sannan daga karshe yace musu :
"SHIN YANZU BA ZAKUYI FARIN CIKI BA, SAURAN MUTANE ZASU KOMA GUDAJENSU DA AWAKI DA TUMAKAI DA ZINARE DA AZURFA, KU KUMA ZAKU KOMA GIDANKU TARE DA MANZON ALLAH!!!".
Sai s**a fashe da kuka suna cewa "Munyi farin ciki mun yarda da Manzon Allah (S.A.W) Shine rabonmu, shine kasonmu!!".
Allah yi salati da amincinka mafi girma bisa Annabinka mafi daraja, Shugaban mutanen farko dana karshe, mai tutar godiya aranar tsaiwa, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa masu daraja da Sahabbansa madaukaka da dukkan mabiya bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Amin Ya Hayyu Ya Qayyum π