Pantamiyya Reporters

Pantamiyya Reporters Awareness

DA DUMI-DUMI: Gidauniyar Farfesa Pantami Ta Ƙaddamar Da Raba Kayayyakin Abinci Fiye Da Buhu 12,500 Da Kuma Kuɗi Naira Mi...
27/02/2026

DA DUMI-DUMI: Gidauniyar Farfesa Pantami Ta Ƙaddamar Da Raba Kayayyakin Abinci Fiye Da Buhu 12,500 Da Kuma Kuɗi Naira Miliyan 33,750,000 Ga Malaman Addini A Gombe

Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami (PIP Foundation) ta ƙaddamar da raba kayan abinci kusan buhu 12,500 da s**a haɗa da shinkafa, masara, gero, s**ari, taliya (spaghetti da macaroni), da sauran su a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.

Aikin raba kayayyakin abincin yana gudana ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Ahmad Walama (Sarkin Malaman Gombe), Dr. Abubakar Saidu (Tsohon babban daraktan asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe), Arch. Dahiru Saidu, da kuma uwar gidan Farfesa Isa Pantami, tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki, matasa, da mata.

Kayan abincin da ake rabawa sun haɗa da buhu 3,500 na shinkafa mai nauyin 50kg, buhu 1,000 mai nauyin 25kg, da kuma fiye da buhu 2,000 mai nauyin 10kg. Bugu da ƙari, akwai fiye da buhu 1,000 na gero da buhu 1,000 na masara. Sauran kayan sun haɗa da buhu 900 na kus-kus, fiye da buhu 2,500 na semovita, katan 500 na macaroni, da kuma fiye da buhu 150 na s**ari.

Ana raba waɗannan kayayyaki ne ga shugabannin addini, shugabannin al’umma, ‘yan siyasa, matasa, mata, marayu, da kuma mutane masu buƙata ta musamman. Kwamitin raba kayan ya tabbatarwa da jama’a cewa za a raba abincin ne a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, sai dai saboda yawan jama’a, ba kowa ne zai iya samu ba, sai waɗanda Allah ya ƙaddara suna cikin jerin waɗanda za su amfana.

Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya shafe shekaru da dama yana tallafawa jama’a a lokacin watan Ramadan, inda adadin tallafin yake sauyawa shekara bayan shekara. Waɗanda s**a amfana sun nuna godiyarsu ga wannan karamci wanda ya kawo farin ciki ga iyalansu, sannan sun yi wa Farfesa da tawagarsa addu’ar Allah ya saka musu da mafificin alkhairi.

Gidauniyar Farfesa Isa Pantami (PIP Foundation) ta ware zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 33,750,000 domin tallafawa malaman addini a Gombe. Gidauniyar ta daɗe tana tallafawa malaman addini a Gombe da ma Najeriya baki ɗaya. A shekarar da ta gabata, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ta hanyar wannan gidauniya, ya tallafa wa malaman Gombe da Naira miliyan 27 a jihar Gombe kaɗai, baya ga sauran tallafi. Dr. Umar Garba Dokaji ne yake jagorantar aikin raba tallafin ga malaman addinin.

22/02/2026
Saqon Abba Sani Pantami  ga mutanen mu!!!Dan Allah indai Professor Isa Ali Pantami  kake so kake karewa a kafar Nan ta m...
22/02/2026

Saqon Abba Sani Pantami ga mutanen mu!!!

Dan Allah indai Professor Isa Ali Pantami kake so kake karewa a kafar Nan ta media kayi haquri karka zagi kowa ko k**a sunansa sabida Azumi,

Kowa yasani daure shaidanu ake wannan wata, to kar shaidan na cikin mutane ya rinjayeka yakai Dan Median malm me Daraja!

Tabbas Babu Dadi Amma inaso munsani duk randa kaji shiru andaina maganan maigidanmu to haqiqa Muna mawiyacin Hali, Amma wancan yace wannan ma yace shine tabbachin megida Yana kan hanya ta nasara,

Kuyi haquri matasa masu yi da kudinsu ba jiran a Basu a daukesu hotoba, ku daure kar haushin karnuka ya hanaku zuwa inda kuka nufa dan inganta rayuwa,

Daga qarshe Muna miqa godiya ga dukkanin wani masoyin malam, a wannan wata malam yana buqatar Adduoinmu fiye da kareshi a ko Ina nagode,

✍️ Bashir Abubakar vice chairman Pantami Social Media Team - PSMT 5th Ramadan 2026

15/02/2026
13/02/2026

Ina Gombawaa ?

Idan akace ku zabi cancanta cikin mutane hudun nan masu neman takarar kujerar Gomna wa zaku zaba ?

Akafta.....

Zuwa ga masu zagi, cin mutunci, Hassada da kazafi ga Professor Isa Ali Pantami Zuwa yanzu na kara tabbatar da In Allah y...
11/02/2026

Zuwa ga masu zagi, cin mutunci, Hassada da kazafi ga Professor Isa Ali Pantami

Zuwa yanzu na kara tabbatar da In Allah ya yarda, shiga siyasar Professor Isa Ali Pantami, Alkhairi ce.

Idan na wayi gari naga mutanen banza suna ta yiwa Malam karya, sharri da kazafi sai naji ina kara kaunarshi, saboda shi kullum da budaddiyar zuciya yake mu'amala na rayuwa da kowa, kuma duk abunda aka tunkara indai mutanen banza suna s**arshi to tabbas alama ce ta Alkhairi.

Wasu suna zagin Malam saboda bakar Hassada kuma bi'iznillahi bakar Hassadar nan itace ajalinsu, domin kullum za ku yita ganin Nasarar shi ne.

Wasu suna zagin Malam don kawai baya bangarensu a siyasance.

Wasu suna zagin Malam don kawai basa goyon bayanshi ya shiga siyasa.

Wasu kuma dabi'arsu ce duk inda s**a ga mutumin kirki sai sun zage shi.

Ina bawa dukkanninsu shawara da su sani, wallahi duk zagi, kazafi, cin mutunci da Hassadarsu duk a banza, bi'iznillahi ba zata taba yin wani tasiri akan shi ba, saidai ta kara mishi soyayyar al'umma.

Domin kowa ya sani wanda aka fi yiwa Hassada shine yake fin kowa yin Nasara da samun cigaba.

Abba Sani Pantami

PANTAMIYYA A BILLIRI: Daruruwan matasa magoya bayan Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya kuma Wazirin P...
07/02/2026

PANTAMIYYA A BILLIRI: Daruruwan matasa magoya bayan Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya kuma Wazirin Pantami) sun gudanar da taro a karamar hukumar Billiri, jihar Gombe.

A yayin gudanar da taron an kara wayar da kan matasan kan abunda ya shafi harkar rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da wayar da kansu.

Haka zalika matasan Billiri sunyi kira tare da roko ga Professor Isa Ali Pantami da ya daure ya fito takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.

Mutanen Billiri sunyi dan-dazo Mazansu da matansu sun fito daga kowane yanki na fadin karamar hukumar, domin nuna soyayya da kaunarsu ga Majidadin Daular Usmaniyya.

Wannan yake kara nunawa da tabbatar da cewa mutanen jihar Gombe na kowane yanki a shirye suke, domin bada gudummuwarsu na ganin Professor Isa Ali Pantami, ya zama Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.

Abba Sani Pantami

Address

Gombe

Telephone

+2349036837383

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Pantamiyya Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Pantamiyya Reporters:

Share

Category