27/02/2026
Tinubu ya dakatar da sallamar manyan jami’an ƴansanda 30 bayan naɗin sabon mukaddashin IG
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da shirin tilasta wa manyan jami’an rundunar ’yansanda kusan 30 yin ritaya, bayan sauyin shugabanci da aka samu a hedikwatar rundunar k**ar yadda jaridar Sahara Reporters ta rawaito.
Matakin ya biyo bayan miƙa ragamar aiki da tsohon Sufeto Janar na ’yansanda, Kayode Egbetokun, ya yi ga wanda ya gaje shi a matsayin mukaddashin Sufeto Janar, Tunji Disu.
Naɗin sabon mukaddashin IGP ya sake tayar da muhawara a faɗin ƙasa kan al’adar da ake bi a rundunar, inda sauyin shugabanci kan haifar da tilasta wa manyan jami’ai, musamman Mataimakan Sufeto Janar (DIGs) da Mataimakan Sufeto Janar na Musamman (AIGs), yin ritaya domin daidaita tsarin jagoranci.
Rahotanni sun nuna cewa an tsara wani shiri da zai kai ga sallamar kimanin DIGs da AIGs 30 bayan sauke Egbetokun daga muƙaminsa. Sai dai an ce Shugaba Tinubu ya shiga tsakani domin dakatar da aiwatar da shirin, lamarin da ya kawo sauyi a cikin tsarin da aka saba.
Wata majiya ta ce matakin shugaban ƙasar ya kawo kwanciyar hankali a tsakanin manyan jami’an rundunar, musamman ma waɗanda ake zargin za su fuskanci ritaya ta dole.
A cikin jerin sunayen da ake yaɗawa a rundunar, an ambaci cewa akalla DIGs takwas ne ake sa ran za a yi wa ritaya domin daidaita sabon tsarin jagoranci. Daga cikinsu akwai Yahaya Abubakar, Adebola Hamzat, Adebowale Williams, da Frank Mba.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, rundunar ’yansanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan dakatar da shirin ba.