02/12/2023
ALHAMDULILLAH MASHA ALLAH🙏💕
MAI MARTABA SARKIN JAMA'ARE YA ZIYARCI SABON COMPANY DA AKE GINAWA NA KHAMJAFA PARBOILED RICE LTD A CIKIN GARIN JAMA'ARE
Cikin Amincewar Ubangiji Yau ya Qaddari Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Jama'are ALH. NUHU AHMED WABI MNI
Yakai Ziyarar Gani da Ido Zuwa Sabon Kamfaninmu na Khamjafa parboiled rice Wanda Alhaji Hassan Usman Khaigaman Jama'are Yake Ginawa Anan Cikin Garin Jama'are.
Mai Martaba Sarkin Jama'are ya ganewa Idonsa Yadda Wannan Aiki Yake Tafiya a Sabon Kamfanin.
Inda Ya Sanyawa Wannan Aiki Albarka Tare da Nuna Farin Cikinsa Matuka Ta Yadda Ake aikin Gadan Gadan Domin Cigaban Wannan Gari namu na Jama'are.
Muna Godiya Kwarai Dagaske Mai Martaba Bisa Wannan Ziyara daka Kawo mana Domin Kuwa Hakanma Ba Karamar Nassara bace.
Daga Karshe Ina Mai Karewa da Addua'ar Allah Ubangiji ya Sanyawa Wannan Company Namu Albarka tare da Nassarori Ameeen ya Hayyu ya Qayyum🤲🤲🤲