25/02/2026
Mutane da yawa suna min magana a Inbox cewa suna son shiga stock market amma abu daya da nake so mu fahimta tun farko shine shiga stock market ba kawai bude app bane, ayi register, a siya share, sannan a jira farashi ya tashi a siyar ba.
Stock market ilimi ne mai zurfi wanda yake bukatar fahimta, nazari da kyakykyawan tsari, duk wanda ya shiga kasuwa ba tare da ilimi ba, zai shiga ne da babban probability na rasa jarinsa.
Stock market tsari ne na cinikayyar hannayen jari na kamfanoni da ake yi a karkashin kulawar doka, a nigeria ana gudanar da kasuwar ne ta hannun Nigerian Exchange Limited inda kamfanoni kamar MTN Nigeria, Dangote Cement da Jaiz Bank suke ba jama’a damar mallakar hannun jari.
Amma kafin ka sayi kowanne share, dole ne ka fahimci cewa farashi ba ya motsi haka kawai, akwai muhimman abubuwan guda biyu da suke tafiyar da kasuwa wanda sune demand da supply. Ma'ana idan masu saye sun fi yawa, farashi zai tashi, idan kuma masu sayarwa sun fi yawa, farashi zai sauka. Shi kuma irin wannan motsin ba'a gane shi da zato ko jita-jita ana bukatar ilimi na musamman da ake kira Technical Analysis.
Technical Analysis wata hanya ce ta nazarin motsin farashi ta hanyar amfani da chart domin fahimtar inda kasuwa za ta iya nufa. Wannan ilimi ya samo asali ne daga ka’idodin Charles Dow wanda ya nuna cewa duk wani bayani da ya shafi kasuwa yana bayyana ne a cikin price. Professional stock trader ba ya bin jita-jita yana karanta abin da chart yake fada masa ne. A Technical Analysis akwai muhimman abubuwan da dole ne duk mai son zama trader ko investor ya fahimta:
Na farko, fahimtar market structure, wato yadda farashi yake yin Higher High da Higher Low a lokacin uptrend, ko Lower High da Lower Low a lokacin downtrend. Wannan shine tushen da zaisa ka gane direction na kasuwa.
Na biyu, fahimtar candlestick chart wanda Munehisa Homma ya assasa tun wasu shekaru da s**a wuce. Candlestick yana nuna Open, Close, High da Low, kuma daga nan zaka fahimci karfin buyers da sellers.
Na uku, Support da Resistance. Support wuri ne da farashi yake yawan samun karfin komawa sama, yayin da Resistance wuri ne da farashi yake yawan fuskantar matsin lamba na sayarwa, fahimtar wadannan wurare zai baka damar sanin inda zaka shiga ko fita daga trade cikin kwanciyar hankali.
Na hudu, amfani da indicators kamar Moving Average da RSI wanda J. Welles Wilder Jr. ya kirkira amma professional trader ba ya dogara da indicator shi kadai yana fara fahimtar price action kafin komai.
Abu mafi muhimmanci a stock market shine Risk Management, ba kowanne hasashenka bane zai zama gaskiya, saboda haka dole ne ka sa Stop Loss, ka kiyaye capital dinka, kuma kada ka taba saka duk jarinka a trade daya.
Saboda haka, shiga stock market ba kawai bude app bane ka saya ka siyar, ilimi ne da ake koya kuma a fahimta da kyau domin a samu arziki mai kyau.
Akwai bukatar a koyar da masu son shiga harkar Stock Exchange yadda ake karanta chart da fahimtar market structure.
Karka biyewa hype, ka nemi Ilimi.
Allah yasa mudace.
© Salisu A. Saheel