18/02/2022
Matsayin Kida. Da Waqa A Muslunci
Tattaunawarmu Da Wani Dan Izala
YABO DA GODIYA SUNTABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI GWARGWADON YADDA YA YABI KANSA DA KANSA
YA ALLAH KAYI TSIRA. DA AMINCI
GA MANZONKA ANNABIN ANNABAWA. SHUGABAN FARKO DA KARSHE GWARGWADON MATSAYINSA DA GIRMAN QADRINSA AWAJENKA
DA ALAYANSA DA SAHABBANSA,
DA WANDA S**A BISHI HARZUWA RANAR SAKAMAKO
Bayan Haka
Ni Muhammad Sani Abs
Na Kasance Ina Cikin Tafiya Da Niyyar Inje Wajen Neman Abincine
Wato Inda Nake Sana'ata Ko Ince Kasuwanci. Sai Na Hadu Da Wani
Dan Izala Bayan Mun Gaisa. Dai Dai Wani Shagon Mai Photo Sai Naga Hotonan Wasu Wanda Nasansu Ajikin Kofar Shagon Sai Nace Wai Su Wanane Nan Haka ? To Dama Suna Cikin Zagayen Mauludin Annabi Saww Akayi Hoton. Sai Yace Sune
Kagansu kai Daganin Wannan Kasan Bai Halattaba
Nace Meke Bai Halattaba ?
Yace Kida Da Waqa!
Nace Ahaba Bai Kamata Kafadi Hakan Ba
Sai Yace Haba Muhammad Sani Ai Bai Halattan Bane
Sai Nace Subahanallahi. Kasan Kuwa Ma'anar Abu Bai Halattaba?
Ma'anarsafa Haramun Ne! Kuma Kasan Illar Haramta Abinda Allah Bai Haramtaba Kuwa!? To Kasani Duk Wanda Ya Harmta Abinda Allah Bai Haramtaba. Ko Wani Ya Haramta Masa Abinda Allah Bai Haramtaba Kuma Yanajin Harmcin Abin Ya Kafirta
Sai Yace Ai Shi Yaji Malamaine Sunfada
Kuma Bari Zan Zoma Da Karatun Wani Malami In Turamaka Kaji!
Nace A'a Bana Sonji Saboda Kasani Shi Malami. Yana Iya Fadar Son Ransa Wani Malamin Dan Karyata Abinda Bahaka Yakeba Musamman Malamanku. Saboda Su Akullum Yan Nuna Iyawane!
Amma Ni Ina Da Hujja Akan Hakan Daga Litattafn Magabata. Cewa Waqa Baharamun Bace. Kida Ba Haramun Bane
Sai Dai Kasani Shi Kida. Da Waqa Kamar Hukuncin Kwalbane! Wato kwalba akaran kanta bata da Hukunci. Sai Abinda Aka Zuluba. Acikinta. Idan Anzuba Giya To Kwalbar Giyace. Yanzu Ta Haramta
Idan Anzuba Lemu. Ko Ruwa Yanzu Kwalbar Lemuce. Ta Halatta
To Haka Waqa. Ko Kida Yake. Menene Acikin waqar Zambo. Idan Zanbone. Ko Batsa. Haramunne
Idan Yabone. Ko Kirari. Ya Halatta Muddin Bai Hada Da Saboba
Hujja Akan Halaccin Waqa Kuwa Kaje Kasameni Shago. Ko Kuma Inbaka Abinda Ya Sauwaqa
YA Zo Acikin Littafin. Muhammadur Rida. Wato
MUHAMMADUR RASULULLAHI SAWW
Yace Alokacinda Manzon Allah Saww Yayi Hijra Daga Makka Zuwa Madina
Ayayinda Manzon Allah Saww Yaje Madina. Alokacinda Yafara Da Ginin Masallacinsa Mai Albarka. To Alokacinda Yake Ganin Masallacin Da Shi Da Sahabbansa Suna Dauko Tubali. Su Sahabban Manzon Allah Saww Sunayi Suna Waqa Suna Cewa
ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﻤﺎﻝ ﻻﺣﻤﺎﻟﺨﻴﺒﺮ ~ ﻫﺬﺍ ﺃﺑﺮﺭﺑﻨﺎ ﻭﺃﻃﻬﺮ
Sai Manzon Allah Saww Ya Amsa Musu Da
ﺇﻥ ﺍﻷﺟﺮﺃﺟ ﺮﺍﻷﺧﺮﺓ. ~ ﻓﺎﺭﺣﻢ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻩ
Kaga Alokacinda Suke Wannan Waqar Manzon Allah Saww Yana Cikinsu Bai Hanasu Ba. Sai Ma Ya Mai da Musu Amsa Mai Dadi Mai Faranta Rai
Haka Ma Ya Inganta Daga Sayyidatuna A'ishatu(Rta)tace Alokacinda Manzon Allah Saww Ya Tunkaro Madina. Zai Shiga Sai Mata Da Kana Nan Yara S**a Tareshi.
Bayan Dama Dai Su Mazajen Masu Karfi Matsa Majiya Karfi Ja Rumai. Da Manyan Masu Kudin Garin Da Masu Fada Aji Nagarin Sun Tareshi Cikin Shigar Yaki Tun Abayan Gari S**a Taroshi S**a Bishi Chan Cikin Daji S**a Taroshi
Shine Sayyida Aisha Tace. Mata Da Kanan Yara Sukuma Sai S**a Tareshi Da Kayan Kina Suna Kida Suna Waqa Suna Cewa
ﻃﻠﻊﺍﻟﺒﺪﺭ ﻋﻠﻴﻨﺎ. ~ ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺎﺕ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ
ﻭﺟﺐ ﺍﻟﺸﻜﺮ ﻋﻠﻴﻨﺎ. ~ ﻣﺎﺩ ﻋﺎ ﻟﻠﻪ ﺩﺍﻉ
ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺒﻌﻮﺙ ﻓﻴﻨﺎ. ~ ﺟﺌﺖ ﺑﺎﻷﻣﺮ ﺍﻟﻤﻄﺎﻉ
Wannan Waqar Da Kidan Duk Dalibin Ilimi. Kai Duk Dan Yaronda Yake Zuwa Islamiyya Indai Ana Karanta Sira. A Islamiyyar Sai Ya San Wannan Saboda Littafin Sira Na 1. Na Yara yan Islamiyya Yazo Dashi
Haka Kuma Manzon Allah Saww Yana Da Mawaqa Wanda Duk Masanin Tarihin Muslunci Ya San Da Su
DAGA CIKINSU AKWAI,
(1)HASSANU BIN THABIT
(2) KA'ABU BIN MALIK
(3) ABDULLAHI BIN RAWAH(Rta)
Wannan Duk Sahabban Manzon Allah Saww Ne. Kuma Mawqan Manzon Allah Saww Daga Cikinsu Ma Akwai Wanda Annabi Saww Yayankewa Hukuncin Kisa Tadalilin Waqa Yasa Annabi Saww Yayafe Masa. Akwai Wanda Annabi Saww Yabashi Kyautar Mala'ika Jibrilu Asw
Cewa Duk Sadda Zaiyi Waqa Jibrilu Zai Tai Makamsa Idan Yakakare
Haka Nan Daga Cikinsu Akwai Wanda Annabi Saww Yayiwa Kyautar Aljannah
Akwai Daga Mawaqan Annabi Saww wanda Annabi Saww Yayi Masa Kyautar Zama Dashi A Aljannah
Akwai Wanda Annabi Saww Yayi Masa Addu'A Saboda Waqarda Yayiwa Annabi Saww Yashekara Dari Da Ashirin(120)Hakurinsa ko Daya Bai Fadiba
Hujja
ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺳﻴﺮ ﺃﻋﻼﻡ ﺍﻟﻨﺒﻼﺀ:
ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺳﻴﺮﻳﻦ ﻛﺎﻥ ﺷﻌﺮﺍﺀ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺣﺴﺎﻥ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ
ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺭﻭﺍﺣﺔ
ﻭﻛﻌﺐ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ
Fassara
LALLAI YAZO CIKIN WANNAN LITTAFI MAISUNA (A'ALAMUN NUBLA'I)
IBN SIRRINA YANA CEWA YAKASANCE MAWAQAN
ANNABI (SAWW) SUNE
HASSANU BIN THABIT
DA. KA'ABU BIN MALIK
DA. ABDULLAHI BIN RAWAH(Rta)
Sannan Kuma
ﻗﺎﻝﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻛﻌﺐ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﺃﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﻌﺮﺍﺀ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ،
ﻗﺎﻝ ﺇﻥ ﺍﻟﻤﺠﺎﻫﺪ ﻣﺠﺎﻫﺪ ﺑﺴﻴﻔﻪ. ﻭﻟﺴﺎﻧﻪ
ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ (ﻟﻜﺄﻧﻤﺎ ) ﺗﺮﻣﻮﻧﻬﻢ ﺑﻪ ﻧﻀﺢ ﺍﻟﻨﺒﻞ
ABDURRAHMAN DAN KA'AB(Rta)
YACE DAGA BABANSA KA'ABU
YACE: YA ANNABIN ALLAH(SAWW)
LALLAI ALLAH YASAUKAR DA ABUNDA YASAUKAR AKAN MAWAQA,
SAI YACE MUJAHIDI YANAYIN JIHADINE DA TAKOBI KUMA DA HARSHENSA. NARAN TSE DA WANDA RAINA YAKE HANNUNSA ABINDA KUKE JIFANSU DASHI TAMKAR YAYYAFIN RUWAN KIBIYANE.
ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺳﻴﺮﻳﻦ ﺃﻣﺎ ﻛﻌﺐ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﺬﻛﺮ ﺍﻟﺤﺮﺏ ﻳﻘﻮﻝ ﻓﻌﻠﻨﺎ ﻭﻧﻔﻌﻞ ﻭﻳﺘﻬﺪﺩﻫﻢ،
IBN. SIRINA YACE. SHI KA'ABU YAKASANCE YANA ANBATON YAKINE CIKIN WAQOQINSA
ﻭﺃﻣﺎﺣﺴﺎﻥ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﺬﻛﺮ ﻋﻴﻮﺑﻬﻢ ﻭﺃﻳﺎﻣﻬﻢ ،
SHIKUMA HASSANU YANA YIMASU ZAMBO DAKUMA YAKOKIN DA AYYAMUL ARAB
(WATO IRIN KASHINDA S**A BAWA KAFURAI ABAYA.)
ﻭﺃﻣﺎﺍﺑﻦ ﺭﻭﺍﺣﺔ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﻌﻴﺮﻫﻢ ﺑﺎﻟﻜﻔﺮ ،
SHIKUMA BIN RAWA YANA MUZAN TASU DA KAFURCINSU,
ﻭﻗﺪﺃﺳﻠﻤﺖ ﺩﻭﺱ ﻓﺮﻗﺎ ﻣﻦ ﺑﻴﺖ ﻗﺎﻟﻪ ﻛﻌﺐ:
HAQIQA QABILAR DAUS TA MUSULUN TANE SABODA WANI BAITI DA KA'ABU YAYI MASU
YACE.
ﻧﺨﻴﺮﻫﺎ ﻭﻟﻮ ﻧﻄﻘﺖ ﻟﻘﺎﻟﺖ**** ﻗﻮﺍﻃﻌﻬﻦ ﺩﻭﺳﺎ ﺃﻭ ﺛﻘﻴﻔﺎ.
Kaga Kenan Idan Har Haramunne Tayaya Za Ace Manzon Allah Saww Har Yayabesu. Harma Yana Fadin Cewa Suna Yakar Kafiraine. Da Takubba ?
Sai Kuma.
ﺃ ﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺧﺮ ﺝ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﻣﻐﺎﺯﻳﺔﻓﻠﻤﺎ ﺍﻧﺼﺮﻑ ﺟﺎﺀﺗﻪ ﺟﺎﺭﻳﺔ ﺳﻮﺩﺍﺀ،ﻓﻘﺎﻟﺖ ﻳﺎﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪﺇﻧﻰ ﻛﻨﺖ ﻧﺬﺭﺕ ﺇﻥ ﺭﺩﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﺳﺎﻟﻤﺎ ﺃﻥ ﺃﺿﺮﺏ ﺑﻴﻦ ﻳﺪ ﻳﻚﺑﺎﻟﺪﻑ ﻭﺍﻟﻐﻨﻰ،ﻗﺎﻝ ﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﻧﺬﺭﺕ ﻓﺎﺿﺮﺑﻲ ﻓﺠﻌﻠﺖﺗﻀﺮﺏ، ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢﺭﻭﺍﻩ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
HAQIQAA YA INGANTA
MANZON ALLAH(SAWW)
YAFURTA ACIKIN SASHIN YAQOQINSA AYAYINDA YADAWO DAGA YAQI
WATABUDURWA BAQAR FATA TA TARESHI(SAWW),
SAI TACE YA MANZON ALLAH (SAWW) HAQI QAA NINAYI BAKANCE NA YIWA ALLAH ALLQAWARIN CEWA
HAQIQA IN ALLAH YADAWO DA KAI LAFIYA DAGA WANNAN YAKIN
SAI NAYI KIDA DAGANGA AGABANKA,
KUMA NAYI WAQA. SAI ANNABI(SAWW) YACE: IN DAI HAR KIN KASANCE KINYI BAKANCE TO KICIKA
KI KADA,
SAI KUWA TAKAMA KADAWA
(HADISIN INGANTACE)
CEWAR MANZAN ALLAH(SAWW)
GA WANNAN MATA(KADA)BABU SHAKKA UMARNINE DA YIN KIDA, DOMIN KUWA DAKIDA AYABI, MANZANALLAH HARAMUNNE
TO WALLAHI DA MANZAN ALLAH(SAWW)Bai ce DA ITA KADABA,
SABODA MANZON ALLAH SAWW
BAYA UMARNI DA MUMMUNa
KO YAYA KUWA ABIN YAKE
KUMA YIN KIDANNAN AGABAN MANZON ALLAH SAWW. YANUNA ZA A' IYA YIN KIDA AGABAN KOWANE MALLMI, DOMIN KOWAYE SHI, MANZAN ALLAH SAWW YAFISHI AMMA GASHI ANYI AGABAN MANZON ALLAH SAWW
Dan. Haka Ni Shawarar Da Zan Baka Kakiyaye. Irin Wannan Maganar
Kasani Akwai Hadisai Ni Kaina Wanda Nasani Suna Dayawa. Da Suke Magana Akan Waqa. Da Kida Kuma Agaban Manzon Allah Saww
Da Wandama Manzon Allah Saww Yasa Akayi Masa. Da Wanda Aka Nemi Iznin Ayi Gabansa Yace ayi
Dan Haka Kakiyaye Wannan Sunnace Idan Ku baku Iyawa Baku Da Masu Basirarda Zasuyi To Kudaina Zagi. Da Kafirtawa
Yanzu Idan Kazagi Maso Yabon Annabi Saww Yaya Zakayi Da Wannan Sahabban Na Manzon Allah Saww?
Ya Allah Kasanyamana Tsaro Daga Fadar Munan Kalamai Ga Wanda Tabasu Hallakane. Sune Manzon Allah Saww Da Sahabbansa Da Masoyanka. Aduk Inda Suke
Alfarmar Manzon Allah Saww