29/03/2022
SHIN NAWA YA KAMATA NA NEMA IDAN ZANYI KIWON BROILER 100 ?
Wasu kan baro shiri tun rani! Dole na fadi haka domin kiwo na son ayi masa tattalin kudi k**ar yadda ake yiwa noma.
Kyakyawar shiri na chikin abubuwan da kansa ayi kiwo cikin nasara.
Kudin kiwo ya ka su izuwa gida biyu : Fixed cost da kuma Variable cost.
Fixed cost shi ne kudin da kayi tattalin su don saye ko kera abinda zaka dade kana morarsa na wani dan lokaci k**ar pen, feeder, drinker, broom, shovel, kerosine lamp da dai sauran su
Amma Variable cost ba k**ar fixed cost ba domin ya kunshi kudin da akayi tattalin su domin sayen abubuwan gudanarwa aduk sanda zaka zuba kaji kana bukatar su, k**ar Day olds, Feeds, Drugs, Vaccines, Saw dust, Fuel ko Charcoal da dai sauran su.
Bayan mun fahimci wannan idan inaso zan zuba broilers guda 100 kudin gudanarwa k**ar nawa ya k**ata nayi tattali ?
Farashin kayayyakin da na lissafo na da bambamci daga gari zuwa gari sannan daga lokaci zuwa lokaci sannan suna hawa da sauka
A yanzu alkalumma da zanyi amfani dasu haka ake sai da su a inda nake da fatan mai Karatu zai fahimci wannan.
Shin idan na zuba kaji broilers 100 buhun abinci nawa za su ci a makonni takwas ?
Za su ci starter 88.18kg ( Buhu 4) sannan za su finisher 413.18 ( Buhu 13).
Starter ( Farashin Buhu 1 #5,850 * buhu 4= #23,400)
Finisher ( Farashin Buhu 1 #6,380 * Buhu 13= #82,940)
Day old #580 * Guda 100= #58,000
Vaccines: Gumboro da lasota guda bibbiyu : #500+ #600= #1100*2= #2200
Drugs: Multivitamins, Antibiotics, Anticoccidiosis guda bibbiyu= #5000
Transportation= #2000
Fuel/ Kero= #3000
Fuel/ Kero= #3000
Total = #176,540
Wanda ke so ya zuba broilers guda 100 sai yayi tattalin kudin gudanarwa akalla #176,540.
Ana iya samun fiya da ko akasi na wannan lissafi wannan ya danganta ga irin kwarewar ka ko ilmin kiwo da kake da ita
Kada a manta ya wancin kajin yanzu muna fitar da su ne a makonni 6 ba 8 ba , don haka idan mako 6 ne kudin zai ragu matukar gaske sannan mai karamin karfi iri na sai ya zub