Amina Lawal Muhammad

Amina Lawal Muhammad Accounts management || Meta sponsored ads || Audit || Consultations || Graphics designing || Adverts || Virtual Classes

+234(0)8067187575

Agriculturist||Social Media Manager||Virtual Tutor

Babu alherin da za ka yiwa ɗanka ko ƴarka a rayuwa fiye da fara kai shi Islamiyyah a farkon rayuwarsa kafin ya fara boko...
29/10/2025

Babu alherin da za ka yiwa ɗanka ko ƴarka a rayuwa fiye da fara kai shi Islamiyyah a farkon rayuwarsa kafin ya fara boko. Islamiyyah ɗinnan tana da matuƙar muhimmanci a farkon rayuwar yaro. Yaro ya san wanene shi, menene ma asalin dalilin zuwansa duniyar.

Allah ne Yake shirya bawa. Ba tare da shakkar haka ba, idan yaro yayi dacen Islamiyyah, gaskiya hakan yana gina masa wata alaƙa ta musamman da Allah. Tun ɗanka yana yaro za a sanya masa tsoron Allah. Idan kana sauraren yaran Islamiyyah ƴan shekaru 5 zuwa 7, za ka ga ko ƙarya wacce ta zama ruwan-dare-gama-duniya ba sa yi.

Duk da tsamin bakinsu sak**akon suna cigaba da koyon magana, za ka ji suna yawan magana gameda Allah Yana da Al-Jannah wacce yake sanya mutanen kirki cikin ta. Kuma Allah Yana da wuta wacce Yake sanya mutanen banza cikin ta. Don haka aƙalla malaminsa ko malamarsa a Islamiyyah ta faɗa masa cewa ƙarya da rashin sallah manyan matsaloli ne da suke kai mutun wuta. Faɗin gaskiya da yin sallah kuma suna kai mutum Al-Jannah. Idan ya dawo gida, ya ji kaima maganganunka gameda Allah ne, da Al-Jannah da Wuta, to tun daga nan kana sanya masa tsoron Allah, da kwaɗayin Al-Jannah.

AlhamdulilLahi, waɗannan malamai na yara sun san yadda suke siffanta musu Al-Jannah da Wuta su zauna a ƙwaƙwalensu sosai. Sun iya yaren yaran. Duk yaron da ka masa irin wannan ginin, ina ganin ko da zai lalace gaba ɗaya nan gaba, to aƙalla wannan tsohon ginin da aka masa a farkon rayuwarsa zai taimaka masa wajen sauraren wa’azi, don ya tuba. Wannan shimfiɗar ka tabbatar ka yi shi tun kafin yaro ya je boko. Ko kuma aƙalla ka sanya shi a boko wanda ake haɗa biyun, kuma a wannan gaɓar ka tabbatar ilimin addinin da ake yi a wajen na gasken ne, ba wai wani Islamic Studies na turanci-turanci sama-sama haka ba.

Wallahi ahir ɗinka sanya yaro a makarantar missionary a wannan gaɓar ta rayuwarsa. Ina tabbatar maka yaronka zai taso a gagara gane ina ya sanya gaba gameda addini, domin za su shayar da shi guba na shaƙuwa da kafirci, kuma amayar da wannan gubar zai masa wahala iya rayuwarsa. Mafi ƙarancin abinda zai zama shine riƙaƙƙen ɗan Boko Aƙida; in ba haka ba kuma ya zama wani musulmi a suna, amma a ayyukansa sai ka nemi musulinci gaba ɗaya ka rasa. Wallahi Sallah kanta sai ta masa wahala.

Me yasa sallah ba za ta masa wahala ba? Kana tsammanin makarantar missionary ne za su koyawa ɗanka sallah? Kai baka san cewa daga shekaru 7 ne aka ce a umurci yaro yayi sallah ba? To ɗanka bai je Islamiyyar kirki ba kafin cika shekaru 7; sai na tambaye ka yanzu: idan ya tashi sallah a shekaru 7 ɗin, wacce Fatihar zai karanta? Wacce Missionary school s**a koya masa? Su sun iya Fatihar ne? Sun iya tasbeehin ruku’u ne da na sujuda? Sun iya tahiya? To ka ga amfanin tura yaro Islamiyyar kirki kenan a farkon rayuwarsa. Bakinsa kawai ya buɗe da duk waɗannan. Fatiharsa ta fi maganarsa ma fitowa, saboda tsabar nanata masa da malamar islamiyyarsu take masa.

Daga baya kuma a shekarunsa irin 11 zuwa 15 ɗinnan ya shiga karatukan Zaure, ana koya masa Zuhudu. Nan ma malaman suna nuna masa wannan duniyar fa kayan banza ce, kada ya halaka kansa wajen neman ta. Ya dage wajen neman rabonsa na duniya cikin abinda Allah Ya yarda da shi, domin fa duniyar nan hanya ce kawai na zuwa lahira. Of course zai yi sauran littafan addini: Aƙida, Hadisi, Fiqihu. Amma dai Zaure shine kusan inda zai koyi wannan Zuhudu ɗin, kuma yana buƙatarsa musamman a wannaj duniyar da kowa bashi da lissafi fiye da kuɗi. Don haka wasu sun tare wa sata, neman kuɗi daga hanyoyi na riba (kuɗin ruwa), safarar miyagun ƙwayoyi, giya dss.

Ka tabbatar rayuwar ɗanka ta yi k**a da wannan ko da ɗan kaɗan ne, a shekaru 15 na farkon rayuwarsa. Idan baka masa wannan ginin ba, ka cuce shi gameda lahirarsa. Kuma Allah zai tambaye ka domin ɗanka amana ne. Yadda Allah Ya turo ka duniya ba don komai ba sai don ka bauta masa, to haka ma ɗanka. Don haka da kai da shi wajibi ne tun farko ku san wanene Allah, don ku kiyaye Allah cikin duk abinda za ku yi, domin ku masu komawa ne zuwa ga Allah. Allah kuma zai tambaye ku gameda abinda ku ka yi a nan duniya.

🖋️ Ibrahiym El Caleel

Address

Kabba Road
Kaduna

Telephone

+2348067187575

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amina Lawal Muhammad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Amina Lawal Muhammad:

Share