13/06/2021
A ADDININ SHIA IMAMAI AKE NUFI DA SIFFOFIN ALLAH:
📚 A addinin Shia dukan siffofin Allah, wadanda ya siffanta kanSa dasu Imamai ake nufi. Misali, Allah Yace:
".... Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa." (Quran-3:30). Yan Shi'a sunce Ali ake nufi. Ayar Al-Quranin da tace:
"Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa." (Quran-55:27). Wai Imam Sadiq yace: 'Mune Fuskar Allah...'
📚 A wata ayar Allah Yace:
"Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi." (Quran-2:115). Wai Imam Ridha yace; Ali bin Talib ne ma'anar 'Fuskar Allah' a cikin ayar.
👏 Allah Ya kiyashemu daga addinin Shia.