20/09/2022
BUSHIYA....
*Ku karanta da kyau, kuma a natse...
Bushiya ba ta iya kusantar 'yan uwanta; domin ƙayoyin da s**a mamaye jikinsu sun zamo masu tamkar wata kariya ce, ba wai kariya ga barin maƙiyansu kawai ba, a'a, har da 'yan uwa da abokan arziki...
A lokacin sanyi, da hunturu, idan sanyi ya yi tsanani, iska ta yawaita, dole take sanya bushiyaye su kusanci juna, saboda neman ɗumi, amma fa dole su jure wa zafin s**ar ƙayoyi.. Idan sun ɗan sha ɗumin juna kuma, sai su ƙara ja da baya da juna, ba za su ƙara kusantar juna ba sai idan tsananin sanyi ya ƙara riskar su.. A haka suke kwana suke tashi, wani lokaci su kusanci juna, wani lokaci kuma su yi nesa da juna.. domin idan s**a ce za su dinga zama a manne da juna, to kuwa dole su yi haƙuri da zama cikin miki da rauni masu haifar da raɗaɗi mai tsanani.. Idan kuma s**a ɗauki matakin rabuwa da juna gaba ɗaya, to kuwa mutuwa ce za ta ɗauke su duka, ɗaya bayan ɗaya...
Mu ma mutane haka dangantakar mu take da juna, babu wanda ba shi da ƙayoyin da s**a zagaye shi, amma kuma ba za mu taɓa samun ɗumin juna ba sai mun yi haƙuri gami da juriyar s**ar ƙaya, da raɗaɗinta..
* Duk wanda yake neman abokin da ba shi da aibi, to kuwa shi kaÉ—ai zai mutu..
* Duk wanda yake neman matar da babu naƙasa a tare da ita, ko mijin da babu naƙasa a tare da shi, to kuwa zai rayu gwauro, ko gwauruwa...
* Duk wanda yake neman É—an uwan da babu matsala a tare da shi, to kuwa zai mutu bai kammala bincike ba..
* Duk wanda yake neman É—an uwa makusanci kamili, to kuwa zai yi ta yayyanke zumuncinsa..
Saboda haka dole ne mu yi haƙuri, mu kuma jure wa s**ar da za ta zo mana daga junanmu, domin rayuwarmu ta sami daidaito..
Ba komai ne za ka fassara ba, ba kuma komai ne za ka yi masa bin ƙwaƙƙwafi ba, mutanen da s**a dage sai sun gano asalin "diamond", a ƙarshe sun gano cewa bai wuce gawwayi ba...
Kada ka matsa sai ka bi diddigi mutane, kamata ya yi ka wadatu da alhairin da suke bayyana maka a zahiri, ka bar abin da yake cikin zuciya ga Ubangiji