14/10/2020
***CIKIN 'YA 'YA MATA DA NA SHANU****
Watara ne Shehu yatafi da Saniyarsa Kasuwa zai
sayar, amma tun safe har la'asar ta kusa
ba wanda ya taya, sai ya hadu da wani
abokinsa dan Kasuwar, yace "Shehu har
yanzu baka sayarda Saniyarnan ba ashe?" Shehu yace "Wallahi kuwa, gashi har yamma
tafara yi" Sai yace "Bani Saniyar ka biyoni a
baya" Shehu yace "Toh" ya bashi Saniya yana
binsa abaya. Sai ya dinga kewayawa da ita a
Kasuwa yana cewa "Wa zai sayi budurwar
Saniya mai ciki wata shida?" nan da nan mutane s**a yanyameta, aka sami wani ya
sayeta da daraja fiye da yanda Shehu yake
tsammani, Shehu yayi murna da wannan abu,
yayi godiya ga Abokinsa, ya koma gida cikin
farinciki. Ba'a dade da faruwar wannan
al'amari ba sai wasu Mata masu dalilin aure s**azo gidan
Shehu dan su nemawa wani Mutum auren
'yar Shehu, sai matarsa ta nemi ya basu wuri
dan suyi magana, Shehu yace da ita "Kada ki
kuskura ki furta wata kalma akan wannan
Yarinya, nasamo wata hanya da ake amfani da ita akan kowace irin Kadara da ta ki
sayuwa, ko Macen da bata da manemi, dan
haka zanyi amfani da wannan hanya akan
wannan 'Ya tamu, nan da nan sai kiga
manema sun baibayeta mu aurar da ita mu
huta", Matar Shehu tace a cikin zuciyarta "To Shehu Allah Yasa wannan hanyar taka dai mai
6ullewa ce". Taje s**a gaisa da bakin nan, ta
kira Yarinya ta gaggaishe su sannan tace
dasu "Kafin ince muku komai Babanta yace
yana da wasu 'yan maganganu da zaiyi
muku, don haka sai ku gyaggyara ku nutsu" sannan akayiwa Shehu izini ya shigo. Shehu
Jaha yashigo s**a gaisheshi cikin
girmamawa sannan ya fara musu bayani
cikin nutsuwa kamar haka "TO BA SAI NAYI
MUKU WANI DOGON BAYANI BA, KUNSANI
'YATA DAI BUDURWACE, 'YAR DANGI, MAI ASALI,
MAI TARBIYYA, KUMA BUGU DA KARI TANA DA
CIKI WATA SHIDA" sai fa wannan ta kalli
waccan, waccan ta dubi wannan, daga nan
s**a tashi sum-sum-sum s**a fice batare da
sun sake cewa komai ba. Wani tsokaci da kuyi game da wannan
hikimar da shehu jaha yayi??