07/06/2026
KAMIN KI DAUKI MUTUWAR AURE MATSAYIN MAGANIN MATSALAR AURENKI YAKAMATA KISAN WASU ABUBUWA GAME DA ZAWARCI.
1). Duk duniya babu wani gidan auren da bashi da matsala acikinsa, sai dai ma'auratan su san yanda suke magance tasu matsalar amma duk yanda k**e ganinsu cikin annashuwa akwai wani abu da suke haquri dashi tsakaninsu.
2). Duk yanda k**e tsammanin cewa haquri k**eyi da mijinki shima sai an sami wasu abubuwan da haqurin yakeyi dake (Duk kuwa nagartarki da lalacewarsa)
3). Duk yanda k**e tsammanin babu macen da zata iya zama dashi idan bake ba, wata na can tana fatan Allah ya bata koda irinshi ne domin nata yafishi munanan halaye.
4). Abubuwan nan da k**e fama dasu, sune fa wadanda a kayita baki haqurin su tun ranar aurenku kamin fara faruwarsu.
5). Kaso mafi yawan matan da s**a fita gidajensu saboda matsala, sunyi dana sani sak**akon matsalar da s**a iske a zawarci tafi ta aurensu da ya mutu.
6). Daga randa aurenki ya mutu kika koma gida nan zaki fara fuskantar wata sabuwar rayuwar da baki taba tsammanin kasancewarta ba a rayuwarki : -
* Da ancewa maza ga bazawara zakiga k**ar ance musu ga karuwa.
* Kusan kowa idan zaizo wajenki maganar banza ce a bakinsa (Koda ko tsaran mahaifinki ne a shekaru).
* Qannenki dake ruguguwar zuwa gidanki yanzu zasu koma sufara rainaki saboda kin dawo cikinsu.
* Sabulun wanka da na wanki saiya fara gagararki.
* Iyayenki da s**a haifeki zasu fara jin kyashin ciyar dake (ko da kuwa su s**ace a sakar musu diyarsu) saboda ciyarwa tana da ciwo.
* Zakiga kowa ya fara janye ya'yansa (musamman mata) daga gareki saboda karki kwarkwarar dasu.
* Abokin qaninki ma zai iya zuwa wajenki fira tare dacewa kinsan kila ko a budurwa k**e bazai iya aurenki ba.
* Zaki iya haduwa da nagartaccen matashi wanda ya cancanci ki aureshi amma a hanashi aurenki ace kin masa tsufa (Kuma hakan ne 🙄).
* Idan kina da ya'ya zakiga yan gidanku suna kallon yaran naki matsayin qarin dawainiya.
* Mijinki yaga damar ya kwace yaranki ya mayar dasu qauye saboda ya quntata miki.
* Za'a iya hanaki abinci gidanku kuma kiyi kwalliya kifita bawanda zai tambayeki ina zaki? Wato kin dade baki fara karuwanci ba.🥹
* Idan kika sami komawa gidan mijinki dole kiyi haquri saboda yasan kawai wahala ta maidoki bawai zaman ya'ya ba (Kamar yanda ake cewa).
* Zaki sami kanki cikin quncin da duk duniya zaki rasa wanda zai saurareki kuma ya fahimceki.
* Zaki fara tunanin gara ki yarda ki auri koma wanene yazo wajenki, daga qarshe kila sai kinje ki iske sabuwar matsala saboda duk aure yana dauke da ita.
* Duk inda zakije sai kiga yammata ma sunata tsofewa babu mijin aure inaga ke bazarawar?
Allah muke roqo ya zaunar daku lafiya a gidajenku, sukumu zawarawan Allah yakawo musu mafita. Allah ya bamu mata nagari, yajiqan iyayenmu.
✍️ Ahmad Yusuf Dansarai
21st Dhul-hijja, 1447
7th June, 2026
https://chat.whatsapp.com/DMpiEPpHpbDJUnt3nqyzp2