27/07/2024
MAZA ZALLA GROUP
Na ɗan saukar da murya, ku matso kusa ku ji. Tsakani da Allah duk daɗin Awara da kake ji ko soya milk ka haƙura, har da soyayyen dankali. In kana shan Na'na' shi ma ka bari in don marmari kake sha, yana da ƙarfin da zai iya karya sha'awar namiji nan take. Waken soya kuwa yana ƙunshe ne da sinadarin estrogen wanda mata ke buƙatarsa sosai, don mace in tana yawan shansa da hulba komaina matantakarta zai dawo daidai.
Kai kuwa in kana ta'amuli soya beans estrogen ya taru a jikinka zai far wa sinadarin testosterone da kake buƙata don mazantaka, in abin ya yi nisa za ka sha mamaki, don ƙarfinka zai ƙare, sai ka zo shimfiɗa ka ji ka a kwance, ƙila ma sai an kai lokacin da za ka fara tunanin ko tsafi aka yi maka, wani ya ce aljanu s**a shafe ka. Domin likitoci za su ce maka lafiyarka lau, kai kuma ba ka ga lafiyar ba.
Mai hikima ne zai ce ka bincika abinda kake ci, anan ne matsalar take, shi ma za ka ce ba wani abu da kake ci na daban, bayan kuwa ga su na'an', gurguru, soyayyen dankali, awara da soya milk kullum kana ci. Shi sinadarin testosterone yananan a yalwace a cikin timatiri, in ya zama dole sai ka ci awara sai a yanka shi a ciki, Sami ƙwallon tumatur ɗaya kawai ƙato ka haɗa da kukumba a riƙa zuba maka a shinkafar rana kana ci ko ka ci zalla.
In dai ka bar ɗibar waɗancan abin za ka sha mamakin ƙarfinka yadda zai dawo. Wanda yake shan na'na' in don ƙamshi ne da daɗi sai ya koma girfa (Cinnamon), da habbahan (Cademon), shayinsa zai yi daɗi ko bai sa citta (Ginger) ba. In kuwa ya haɗa waɗannan a shayi ya zuba zuma gaskiya ba za a ce bai da lafiya ba garau zai dawo.
Ɗan matso. Maganin da nake son ba ku shi ne: ku sami albasa, ku raba ta biyu, ku ɗauki rufi guda ku yayyaka ta, ku samo tafarnuwa ku sami kamar sala uku masu girma ku daddatsa ta da wuƙa, sai ku samo kukumba ku wanke, kar a cire komai in ba saman da ƙasan ba. A yayyaka ta a zuba su a bulanda a markaɗe.
Sai a tace, ɗan kofi guda da safe ɗaya bayan abincin dare. Zai dawo maka da ɗan