Fitilar Masoya

Fitilar Masoya Like

19/08/2026
17/08/2026
04/08/2026

Part 2

Idan kina da burin zama mace ta gari ga mijinki, tun kafin aure akwai abubuwa guda bakwai da ya kamata ki fahimta sosai....
03/08/2026

Idan kina da burin zama mace ta gari ga mijinki, tun kafin aure akwai abubuwa guda bakwai da ya kamata ki fahimta sosai.

1. Aure ibada ne.
Aure ba wasa ba ne, ba jin daɗi kaɗai ba ne. Ibada ce da za ta zama hanyar samun yardar Allah idan kika rike ta yadda ya dace. Duk wata mu’amala da mijinki, daga kyautar murmushi har zuwa bauta masa, tana iya zama sadaka a wurin Allah.

2. Mijinki shugaba ne a gare ki.
Shi ne shugaban gidan, kuma Allah ya ɗora masa nauyin jagoranci. Idan kika yarda da shugabancinsa cikin adalci, k**e bawa gidanku kwanciyar hankali da albarka. Kiyayewa da jayayya ba sa kawo komai sai rushewar aure.

3. Kiyi biyayya cikin alheri.
Ba wai a kowane abu ki rufe ido ba, amma ki kasance mai biyayya a cikin alheri da abin da bai saba wa Allah ba. Biyayyarki tana kara masa ƙima da girmamawa a idanunsa.

4. Mutunci da girma ga iyayensa.
Kafin ki zama mata a gidan aure, ki san cewa iyayensa da danginsa suna da matsayi a wurinsa. Ki nuna musu mutunci da girmamawa, domin hakan yana daga cikin ginshikan da ke tsare zaman aure.

5. Ki zama sirrin gidanki.
Kar ki zama mace mai yada matsalolin gida. Komai ya faru tsakaninku, ki zama mai rike sirrin gidanki. Sirrin aure kamar kayan ado ne, idan kika tona shi, kowa zai raina ki.

6. Ki kasance abokiyar tafiyarsa.
Namiji yana bukatar mace mai fahimta, mai iya raba farin ciki da damuwarsa. Ki zama abokiyar shawara, mai ba shi kwarin gwiwa, ba mai ƙara masa nauyi ba.

7. Ki kula da kanki.
Ki tuna, mijinki zai kalle ki a kullum. Ki zama mai tsafta, mai kyau a idanunsa, mai daukar hankali. Idan kika yi sakaci da kanki, ki tuna akwai wanda zai kalla a waje.

Ukty, idan kika fahimci wadannan abubuwa tun kafin aure, za ki samu natsuwa, kuma Allah zai baki mijin kirki wanda zai ɗauke ki da daraja.

Ki sani… mace ta gari rahama ce ga mijinta, kuma kyauta ce daga Allah.

Allah ya datar da mu da zaman aure na alheri. Ameen.

F Ismail oppicial
https://whatsapp.com/channel/0029VbApD4J4inosDEM7ey1l

Sallallahu alaihi Wasallam ❤️🥰💯
03/08/2026

Sallallahu alaihi Wasallam ❤️🥰💯

03/08/2026

KADDARAR SO � fart 1

22/06/2026

Alhamdulillah 😍

JUMA.AT MUBARAK
19/06/2026

JUMA.AT MUBARAK

Wannan shine Allah yasa mudace
19/06/2026

Wannan shine Allah yasa mudace

Address

Yankaba Haye Hotoro
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fitilar Masoya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share