14/05/2026
KI ZAMA ABAR KOYI GA AL’UMMA
Ki zama mace abar koyi ga al’umma, ba wai da magana kawai ba, sai da aiki da halaye nagari. Addini ya koyar da mu cewa darajar mace tana cikin kunya, haƙuri, gaskiya da riƙon amana. Duk macen da ta siffantu da waɗannan kyawawan ɗabi’u, tana haskaka kanta tare da zama fitila ga sauran mata.
Ki kiyaye mutuncinki da darajarki, domin ke tamkar madubi ce ga wasu. Duk abin da kika aikata, akwai masu koyi da ke. Saboda haka, ki zaɓi abin da zai amfani rayuwarki ta duniya da lahira.
Ki tuna, rayuwa ba ta tsaya ga abin duniya kaɗai ba. Akwai hisabi a gobe. Duk wata ɗabi’a da ba ta dace da addini ba, komai sauƙinta a yau, na iya zama nauyi a ranar gobe.
Yawaitar kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba daga kafafen sada zumunta ko abokai na iya lalata tarbiyya. Ba duk abin da kowa yake yi ne ya dace da ke ba. Ki tsaya kan abin da addini da al’ada mai kyau s**a yarda da shi.
Ki sani cewa mace ta gari tana gina al’umma ne ta hanyar ɗabi’arta. Idan mace ta gyaru, iyali ya gyaru; idan iyali ya gyaru, al’umma ta gyaru. Don haka, ki ɗauki wannan matsayi da muhimmanci:
KI ZAMA ABAR KOYI, BA ABAR KALLA BA.
Allah Ya sanya mu cikin mata nagari masu amfani ga al’umma.
Ameen, Ya Hayyu Ya Qayyum.
Fitilar Masoya ✍️