05/10/2022
Shin Kwankwaso Zai Iya Cin Takarar Shugaban Ƙasar Nijeriya?
Bari na bada wani ɗan labari a taƙaice:
“Mafi girman masifar da zata afkawa mutum ba wai ya siyar da ruhinsa ga shaiɗan bane, a'a sam, babbar masifar ita ce mutum ya kaiwa shaiɗan tallan ruhinsa kwatsam kuma shaiɗan ɗin yace ba ya siye.” – Wannan shine sakin layin da Wasily ya buɗe wasiƙar sa dashi, wasiƙar nan dai daya aikawa abokinsa Yanis. Yanis, yayin karanta wasiƙar sai yace a ransa: “ko me ya samu abokina da ya zambaɗo wannan uban karin magana?”
Sai wasiƙar Wasily ta cigaba: “na gama PhD amma duka masana'antu sunƙi bani aiki. Kuma na na jiyo wani malamin tsimi da tanadi yana cewa idan leburanci yayi arha masana'antu zasu yi yunƙurin cin gajiyar arhar don haka sai su ɗauki sabbin ma'aikata. Da jin haka sai na zabtare albashin da nake nema da kaso sittin. Amma har yanzu ban samu aiki ba”.
Sai Yanis yayi murmushi yace: “har yanzu wanna ƙaryar ta arhar lebura tana aiki dama?.......ya kai aminina Wasily, ka ajiye wannan banzar fahimta data mamaye Amurka ƙarƙashin mulkin Reagan, da Birtaniya ƙarƙashin mulkin Thatcher, ka kuma yi amfani da hakan ka san cewa, arhar ma'aikata bata sawa a ɗauke su aiki, imanin za'a samu riba ne kaɗai yake sanyawa a ɗau ma'aikata.......a yanzu kuma cunkushewar al'amura ta sanya gaba ɗaya masana'antu sunyi imani da cewar ko kyauta mutum zaiyi musu aiki bazasu ɗauke shi ba, saboda idan sun ɗauke shi baza'a sayar da abinda aka sarrafa ba don haka baza'a samu riba ba. Don haka ka ƙaddara a ranka yakai aminina, cewa duk tsadar albashinka, idan masana'antu sun yarda za'a ci riba, to wallahi sai sun baka aiki. Haka kuma duk arhar albashinka, idan masana'antu s**a yarda baza'a ci riba ba, toh fa sai dai kayi haƙuri.”
Wannan jidali na masana tsimi da tanadi yayi daidai da yadda wasu mutane ke tambayar: SHIN KWANKWASO ZAI IYA CIN ZAƁEN SHUGABAN ƘASA A SHEKARAR 2023?
Da fari dai, kamar aikin yi a duniyar da Wasily ya rubuto wasiƙa, duk ƙarfin da ɗan siyasa yake ji yana da shi, idan mutane basu yi imani zai iya cin zaɓe ba, to bazai ci zaɓe ba... Ba don komai ba sai saboda wannan imanin ne zai hana su zaɓarsa, kuma da ƙuri'unsu ne kaɗai zai iya cin zaɓe. Haka kuma duk raunin ɗan siyasa, idan mutane s**a yi imanin bazai ci zaɓe ba, to haƙiƙa zai ci, saboda imanin nasu ne zai tunzurasu su zaɓe shi, kuma ƙuri'unsu ne dai za'a lissafa a bashi kujerar.
Cakwakiyar dai kamar abinda Malamin falsafa Rousseau ya faɗa ne akan mu'ujiza. A ra'ayinsa, ita ɗin tana yiwa kanta aiki ne. Da ace Sarki Oedipus, wanda bokaye s**a ce ɗansa zai girma ya kashe shi, ya kau da kai ya raini ɗan nasa da kansa maimakon jefar dashi har maƙiya su tsinta su raine shi ya zamo makashi, ai ɗan nasa bai zamo maƙiyinsa ba har ya kashe shi. Amma da ya jefar, maƙiya s**a tsinta s**a raina, sai jawabin bokaye yayi aiki, ɗansa yazo ya kashe shi.
Ya kai me tambaya a kan Kwankwaso, shin kasan da kai da Sarki Oedipus baku da maraba, haka kuma shaci faɗin ƴan adawa bashi da maraba da zancen bokaye? Idan ka bari aka saka maka shakku akan yiwuwar cin zaɓen Kwankwaso, to tun ana kwankwaso ya faɗi zaɓe, kuma kaine ka kayar dashi. Amma kuma idan shaci faɗin mutane ya ƙara maka imani, ranar gobe dakai za'a haɗu a yiwa bokaye dariya, yayin da shi kuma jagora ke can Villa yana warware ɓarnar da aka yiwa Nijeriya.
Wannan yasa a matsayinka na me burin ganin wani ɗan siyasa yaci zaɓe, in dai har da gaske kake kana so yaci ɗin, kada ka tambaya ko zai iya ci ɗin, kawai kayi imani, ranar zaɓe kuma kaje ka dangwala masa ƙuri'a. A aikace, wannan shine nasara, kamar yadda yakamata mu gane cewa a falsafance, imani shine mu'ujiza ba shakku ba. Shakku rusa ta yake.
Ga masu shakku akan wanda suke burin ya zamo shugaba, sakamakonsu zai zamo kamar masana'antun da s**a hana Wasily aiki ne- asara, da kuma irin goben Sarki Oedipus - mutuwa da bin kunya. Dukkansu mummunar ƙaddara ce zata afkawa burin na su.
Amma kuma g wanda s**a yi imani da yiwuwar zamowar jagoransu shugaba, tarihin Bill Clinton, Barrack Obama, Ibrahim Shekarau a 2003, Rabi'u Kwankwaso a 2011, sun ishe su ishara. Imaninsu ya bawa zancen bokayen dakali kunya! Hakan kuma yasa a komai kayi imani kawai, ka kuma sa wasu suyi, kyakkyawar ƙaddara na nan tafe. Idan kuma kana musu, ranar zaɓe jeka ka cillawa Kwankwaso ƙuri'a ka gani idan bai zamo shugaban ƙasar Nijeriya.
30/09/2022
Lawan M Ahmad Karaye