02/04/2022
RAHOTANNI DAGA MuRYA DUB STUDIO
Barkan ku da jimirin sauraronmu
A yau sabar 2_4_2022 wace tai dai dai da 1 ga watan Ramadan
* Babban masallacin Birnin kano
Tarishi ya nuna cewa masallatan farko da aka fara ginawa a Birnin kano, an ginasu ne a wajejen unguwannin madabo,jujin labu da "yandoya .
A tsakanin shekarar 1463 zuwa 1499, sai sarkin kano Muhammad Rumfa ya gina masallaci a nan jikin gidan makama, inda ya fara zama .
A shekarar 1582 sai sarkin kano Muhammadu babba zaki ya sakewa masalacin mazauni inda yake yanzu.
A shekarar 1911 aka ginawa masalacin hasumiya
Sannan kuma a shekarar 1938 sarkin kano ya bayaro ya rushe Wanda Dabo ya gina aka gina masalacin juma'a na yanzu
* Ramadan gwanin sha'awa
Fasto Buru kaduna ya raba buhunan shinkafa ga mussulmi a masu Azumi.
Wani fitaccen malamin addinin kirista, fasto yohanna buru kaduna, ya raba buhunan shinkafa domin Ramadana ga wasu al'umar mussulmi da suke makwaftaka da shi .
A wata majiyarma an tabbatar da cewa ba wanna bane karo na farko dashi babban malamin addinin kiristan ke raba buhunan shinkafa ga mabukata ba domin watan ramadana.
* A nan kuma gwamnan jahar kaduna Mal. nasur El'rufa'i yayi barazanar kawo sojojin haya daga kasashen domi yakar "yan ta'addan da ke ta'addanci a cikin dazuzzukan jahar kaduna,idan har gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Muhammad buhari ta gaza kawo karshen ta'addanci.
Wanna shine jigon rahotanni mu zaku iya bayyana mana ra'ayinku akai sai munji daga gare ku
A nan muka kawo karshen rahotanni mu na wannan Rana
Ni abdulmalik shehu A.malik jogana nake cewa kuhuta lpy
# MuRYA DUB STUDIO