KGT News

KGT News KGT News na kawo muku sahihan labarai da s**a shafi tsaro da lafiya a Najeriya da duniya baki daya.

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA, na shirin ɗaukar matakin shari’a kan shugaban FIFA, Gianni Infantino, bisa ...
27/08/2026

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA, na shirin ɗaukar matakin shari’a kan shugaban FIFA, Gianni Infantino, bisa zargin gudanar da harkokin kuɗi ba bisa ka’ida ba.

Matakin ya samo asali ne daga wani shirin FIFA da Infantino ya gabatar, wanda zai bai wa masu zuba jari masu zaman kansu kaso a cikin kuɗaɗen kasuwancin gasar Kofin Duniya.

Shirin mai suna FIFA Forward Enterprise, wanda yanzu aka yi watsi da shi, ya haɗa da sayar da kashi 20 cikin 100 na wata sabuwar ƙungiyar da za ta mallaki wasu haƙƙoƙin kasuwancin FIFA ga kamfanin Thrive Capital.

27/08/2026

An kashe soja yayin da dakarun sojin kasar nan s**a dakile hare-haren ’Yan ta’adda a Sokoto

27/08/2026

Me ya sa Koriya ta Arewa ke adawa da makaman da Amurka za ta sayar wa Koriya ta Kudu?

26/08/2026

Yadda gwamnan Kano Abba ya kashe 26.5 wajen tafiye-tafiye da gyaran Ofishin gwamna.

25/08/2026

Dakarun Amurka sun horas da sojojin kasar nan dabarun yaki

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su ƙara kaimi wajen ceto Musulman da ak...
25/08/2026

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su ƙara kaimi wajen ceto Musulman da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja.

An sace mutanen ne bayan kammala sallar Juma’a a wasu al’ummomi na yankin, ciki har da Dekara, inda ‘yan bindiga s**a kai hare-hare a ranar Juma’ar da ta gabata.

Shugaban ƙasar ya umarci Rundunar Soji, ’Yan Sanda, DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ceto su.

25/08/2026

Fiye da mutane dubu 10 aka kashe a Najeriya a cikin shekaru 2.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da dogaro da tsarin rund...
24/08/2026

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da dogaro da tsarin rundunar ’yan sanda da ke karkashin kulawar gwamnati ta tarayya kawai wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara ba.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, yayin wani zama na musamman a taron shekara-shekara na 66 na Nigerian Bar Association (NBA).

Rundunar Sojojin Najeriya da ke gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a jihar Zamfara ta ce ta ceto mutane shida da aka y...
24/08/2026

Rundunar Sojojin Najeriya da ke gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a jihar Zamfara ta ce ta ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, tare da cafke wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai.

Sojojin sun ce sun samu nasarar ceto mutanen ne a wani samame da s**a gudanar a jihar, yayin da suke ci gaba da gudanar da ayyukan da nufin dakile ayyukan ’yan bindiga da masu safarar makamai.

Majalisar Ilimin Shari’a ta ƙasa (Council of Legal Education – CLE) ta dakatar da wasu daliban shari’a biyar daga rubuta...
24/08/2026

Majalisar Ilimin Shari’a ta ƙasa (Council of Legal Education – CLE) ta dakatar da wasu daliban shari’a biyar daga rubuta jarabawar ƙarshe ta lauyanci na tsawon shekaru 10, bayan gano cewa sun aikata magudin jarabawa.

An yanke hukuncin ne a taron majalisar na zangon uku na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ranar 13 ga Agusta, 2026, a hedikwatar hukumar dake makarantar horas da lauyoyi da ke Bwari, Abuja.

Address

Tukuntawa
Kano
700234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KGT News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to KGT News:

Shortcuts

Share