Lafiya medicine store

Lafiya medicine store Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Lafiya medicine store, Business service, Shanono, Kano.

16/04/2022

Masha Allah

31/05/2021
16/10/2020

Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta amince ta biya ƙungiyar malaman Jami'oi ASUU naira biliyan 30 a tattaunawar da s**a yi a ranar Alhamis.
Ana tunanin ɓangarorin biyu sun fahimci juna amma kuma hakan bai sa ɓangaren ƙungiyar malaman ya sanar da janye yakin aikin ba inda ƙungiyar ta sake amincewa su sake zama teburin tattaunawa da gwamnati.
Wata sanarwar da ma'aikatar ƙwadago ta fitar ta ce gwamnati ta amince ta fitar da kuɗi ga jami'o'in.
Sai dai kuma gwamnati ba dukkanin kuɗin za ta ba jami'o'in ba, za ta dinga fitar da su ne kaɗan-ƙadan tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Fabrairun 2022.
An shafe wata shida ɗaliban jami'o'i na zaman gida a Najeriya saboda yajin aikin na ASUU duk da ɗage dokar kulle da gwamnati ta yi.
Baya ga biliyan 30 da gwamnati za ta biya ASUU, bayanai sun kuma ce gwamnati za ta kashe naira biliyan 20 wajen farfaɗo da ɓangaren ilimi a wani ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙarshen yajin aikin na fiye da watanni shida.
Sai dai kuma kan batun tsarin albashi da ASUU ke jayayya da gwamnati akai, ɓangarorin biyu sun samu saɓani akai inda malaman Jami'oin s**a ce sai dai a biya su albashin da suke bi ta tsarin albashin GIFMIS, yayin da kuma gwamnati ta dage kan tsarin IPPIS da ASUU ke adawa da shi.
Cikin wata sanarwa ASUU ta bukaci dukkanin mambobinta su ƙauracewa jami'an IPPIS da ta ce za a tura aikin rijistar malaman a jami'o'i daga ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.
Ƙaramin ministan ƙwadago Festus Keyamo ya faɗa a shafinsa na Twitter cewa za su yi ƙoƙarin shawo kan ƙungiyar ASUU kan batutuwa da dama ciki har da tsarin albashin IPPIS da malaman ke jayayya akai.
Tun da farko ASUU ta nuna cewa tsarin biyan albashin IPPIS, shi ne babbar matsalarta, kuma idan har gwamnati ba ta yi wani abu a kai ba, to malaman jami'oi ba za su janye yajin aikin ba, kamar yadda Shugaban kungiyar ta ASUU reshen Jami'ar Bayero Kano Farfesa Haruna Musa ya shaida wa BBC.

27/09/2020

BUHARI YA FASA KWAI - Karanta ka Raba a shafinka

Dalilin da yasa Najeriya ta shiga cikin Matsalolin Tabarbarewar Tattalin Arziki da Talauci - Muhammadu BUHARI
------------------------

Shugaba Muhammadu Buhari a birnin New York na kasar Amurka, ya sake yin bayani dalla - dalla kan dalilan da ya sa Nigeria ta samu kan ta cikin matsalolin da muke fama da su a yanzu.

Shugaba Buhari yayi bayanin ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu 'yan Nigeria su 15 da s**a yi fice tare da kwarewa a wuraren da suke aiki a kasar ta Amurka, wadanda Babbar Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Kasashen Waje, Mrs. Abike Dabiri-Erewa ta jagoranta s**a gana da Shugaban Kasar.

Ganawar ta bawa Shugaba Buhari damar yi musu bayanin dalla-dalla kan dalilan da ya sa 'yan Nigeria da kasar ke cikin wahalhalu a yanzun, sai dai ya basu tabbacin cewa idan dukkan 'yan Nigeria zasu bada gudunmawarsu ciki harda mazauna kasashen waje, Kasar za sake daidaituwa har ma a koma fiye da yadda ake a baya cikin lokaci ba mai tsawo ba.

Ga bayanin na Shugaba Buhari wanda ya ratsa zukatan duk wadanda suke wurin ganawar...

"Na yi matukar farin cikin wannan ganawa da ku, duk inda ka je a fadin duniya, za ka samun 'yan Nigeria na kwarai kuma hazikai da s**a yi fice ta fannoni daban - daban. Kuma ba suna amfanar kasar da suke zaune ne kadai ba, mafi yawan lokuta suna taimakawa Nigeria musamman a bangaren tattalin arziki.

"Mun shiga matsalolin da muke ciki a yanzu saboda ba mu yi tanadi domin lokaci makamancin wannan ba. A misali, daga shekarar 1999 zuwa 2015, a lokacin da muke iya samar da danyen mai ganga milyan biyu da rabi a kullum kuma farashin danyen man ana sayar da shi fiye da dalar Amurka $100, ba mu yi tadani ba, kuma ba mu samar da ayyukan da zasu ciyar da kasar nan gaba ba. Cikin kankanin lokaci a yayin da muka zo a 2015, farashi danyen mai ya fadi zuwa kasa da dalar Amurka $30.

"Na tambaya, ina tanade - tanaden da muka yi domin irin wannan lokaci? Sai aka ce Babu komai, ba mu yi tanadin komai ba. Na sake tambayar ina hanyoyin jiragen kasa da tituna da zasu saukaka mana rayuwa a irin wannan lokaci? Wadanan ma babu. Na sake tambaya, me da me muka yi da biliyoyin dalolin da muka tara cikin wadannan shekaru? Sai s**a ce wai sun sayo abinci. Abinci na biliyoyin daloli? Ban yarda da su ba kuma ba zan taba yarda ba.

"A mafi yawan yankunan Nigeria, muna cin abin da muka noma ne. Mutanen Kudu suna cin gari ne, wadanda suke Arewa suna cin gero ne, wanda su s**a noma shi, kuma wannan abincin da suke nomawa ya kai akalla kaso 60% na abin da muke ci. Saboda haka, ina biliyoyin dalolin s**a tafi? Mun yi wa kan mu matukar barna, mun ki ciyar da kasar mu gaba a lokacin da muke da makudan kudade.

"Idan za mu yi maganar jami'an tsaron mu ne, sun samu daraja, ana girmama su, saboda kokarin samar da zaman lafiya da s**a yi a kasashen kamar su Burma, Zaire, Sudan, Liberia, Sierra-Leone, kawai cikin kankanin kokaci wadannan jami'an tsaro sai s**a kasa kawo kananan hukumomi 14 daga cikin 774 da muke da su daga hannun 'yan Boko Haram. 'Yan ta'adda sun gagare su, har sai lokacin da muka zo, muka hargitsa su, muka nakasa su, muka rage musu karfi tare da kwato duk wuraren da suke hannun su.

"Kafin mu zo, Boko Haram suna yin abin da suke so, suna kashe mutanen da basu ji ba, basu gani ba a masallatai, majami'u, makarantu, kasuwanni da tasoshin motoci da sauran su. Kuma suna kiran Allahu Akbar, kuma idan har da gaske sun san Allah ba zasu taba yin irin wadannan ta'addanci ba. Musulunci ko kowane addini da na sani ba, bai yarda da ta'addanci ba. Amma sun kashe dubban mutane da sunan addini. Yanzu mun yi maganin wannan ta'addancin.

"Haka kuma wadanda s**a sace dukiyar Nigeria ba sa cikin farin ciki, sun dauki tsageru a yankin Niger Delta, suna yi mana zagon kasa ta hanyar farfasa hanyoyin mai. Muna yin asarar miliyoyin gangar danyen mai a kullum, a lokacin da duk dala dayan da muka samu tana da amfani. Kuma abin haushi ne a ce jihohi 27 daga cikin 36 da muke da su a Nigeria ba sa iya biya albashin ma'aikata.

"Nayi addu'a sosai, Allah ya bani Shugaban Kasa, na tsaya a 2003, 2007, 2011 da kuma 2015, Allah ya amsa addu'a ta. Ku kalli abin da nazo na samu a kasa. Amma ba zan yi nadama ko korafi ba, tunda na roki Allah ne kuma ya bani. A aikin Soja, na samu karin matsayi daga Laftana zuwa Manjo-Janar. Na rike matsayin Gwamna a 1975 a jihar da a yanzu ta haifar da jihohi 6. An daure ni na tsawon shekaru 3, na kuma rike mukamin Shugaban PTF, wanda a lokacin take da naira bilyan 53 a asusun ta.

"Allah ya albarka ce ni sosai, so ba zan taba nuna damuwa ta ko korafi ba. A duk sanda wani ya zalunci ne, ina rokon Allah ne ya bani ikon yafewa. Allah ya bani abubuwa masu tarun yawa.

"Sannan ku tuna, bayan shekaru 16, Jam'iyya guda na mulki, ba jam'iyyar da za ta zo ta samu abubuwa cikin sauki, haka halin Dan Adam yake. Muna bukatar nagartattun hannaye su rike Nigeria, kuma zamu yi amfani da wadanda suke da su a yanzu. Za su na gayyace ku ku dawo gida idan lokacin yayi, saboda haka ina so ku zama cikin shiri."

Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wannan jawabi na sa mai matukar ratsa jiki, dukkan wadannan s**a halarci zaman sun tabbatar da cewa a shirye suke don bada gudunmawarsu don ganin kasar su ta gado ta ci gaba ta kowane fanni.

— Bashir Ahmad,
Maitaimakawa Shugaba Buhari
Kan Sababbin Kafafen Yada Labarai
(Social Media).

Address

Shanono
Kano

Telephone

+2348117277561

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lafiya medicine store posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Lafiya medicine store:

Share