27/11/2025
Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!
Muna mika ta'aziyyar rasuwar babanmu, Shaykh Dahiru Usman Bauchi zuwa ga dukkan iyalansa, da dalibansa, da yan'uwansa da dukkan jama'ar da wannan rashi ya shafa. Muna karanta
إنَّ لِلَّه ما أَخَذ ولَهُ ما أَعطَى، وكلُّ شَيءٍ عِنده بِأجَل مُسمَّى
Muna rokon Allah (SWT) Ya yafe masa kura-kurensa, Ya sanya Aljannah ce makoma gare shi. Allah Ya bada ladan hakuri.