Abdurrashid Umar Muhammad

Abdurrashid Umar Muhammad Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdurrashid Umar Muhammad, Business service, Kano.

30/07/2025

RASHIN IYA RUBUTU MU'UJIZA CE A GARE SHI:

Rashin iya rubutu da rashin iya karanta rubutu mu'ujiza ce ga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Watau Allah ne kawai Yake masa wahayi shi kuma sai ya haddace Wahyin cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa sannan ya karanta wa sahabbansa abin da ya haddacen.

Lalle da Annabi ya iya rubutu da karatu da kafurai da munafukai za su ƙara samun karfin guiwar tuhumar sa da cewa wasu littattafai ne ya ke karantowa sannan ya yi ikirarin cewa wahiyi ne Allah Ya yi masa.

Allah Ya ce cikin Suratul Ankabut aya ta 48: ((A gabaninsa ba ka kasance kana karanta wani littafi ba, ba ka kuma (kasance) kana rubuta shi da damarka ba, da kuwa (hakan ya faru to da) da Mutanen banzan sun yi shakka)). وما كنت تتلو من قبله من كتاب ولا تخطه بيمينك اذا لا ارتاب المبطلون.

Kafuran zamanin Annabi mai tsira da amincin sun yadda da cewa bai iya rubutu ba; wannan ma shi ne ya sa s**a yi masa ƙage s**a ce: Alƙur'ani wasu tatsuniyoyi ne da shi Annabi ya nemi wasu su rubuta masa sannan kuma a riƙa koya masa su da baki yana haddacewa safiya da maraice! Allah Ya hikaito maganarsu a cikin Suratul Furƙan aya ta 5 Ya ce: ((S**a ce tatsuniyoyin mutanen farko ne ya nemi a rubuta masa su, waɗanda ake koya masa da baki safiya da maraice)). وقالوا أساطير الأولين اكتتبها فهي تملى عليه بكرة واصيلا.

28/07/2025
25/12/2024

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
LALLAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MUNA GODE MASA MUNA NEMAN TAIMAKONSA MUNA NEMAN GAFARAR SA MUNA NEMAN TSARI DA ALLAH DAGA SHARRIN KAWUNANMU DA MIYAGUN AYYUKANMU WANDA ALLAH YA SHIRYE SHI BABU MAI BATAR DASHI KUMA WANDA YA BATAR BABU MAI SHIRIYA YASA INA SHAIDAWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH SHI KADAI BA SHI DA ABOKIN TARAYYA KUMA INA SHAIDAWA CEWA MUHAMMAD BAWANSA NE KUMA MA,AIKISA NE TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI DA ALAYENSA DA SAHABBANSA DA WADANDA S**A BI SUNNARSA HAR ZUWA RANAR SAKAMAKO AMIN

23/09/2024

Address

Kano

Telephone

+2347037373069

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdurrashid Umar Muhammad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abdurrashid Umar Muhammad:

Share