19/04/2023
Yanzu Alhasan Ado Doguwa Zai iya gogayya da Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE a Siyasance ?
Yakamata kwankwaso Ya Lura Da Abubuwan Da Suke Kai Komo A Tarihin Siyasar Sa, Musamman Abinda Ya Shiga Tsakaninsa Da Wannan Bawan Allah, Hakika Kwankwaso Ya Nunawa Jama’a Yana Da Wata Kima Ta Daban Wadda Sauran Jama’a Sukan Kalleshi Da Ita, Zan Ja Hankalinsa Da Ya Tuna Cewa A Yanzu Yar Manuniya Ta Nuna Cewa Hon Alhassan Ado Doguwa Zai Iya Ja Da Shi Kuma Ya Kai Labari, Saboda Haka Yakamata A Tsaya Ayiwa Tufkar Hanci Domin A Haifarwa Da Arewacin Nigeria Da Mai Idanu.
Kano Ta Kudu Gabadaya Muna Iya Cewa Kwankwaso Yaci Dukkan Akwatunan Sa Amma Banda Akwatunan TudunWada Da Doguwa Wannan Shine Yake Kara Tabbatar Da Jajurcewar Dan Ado A Wannan Yanki, Saboda A Gani Na Da Kuma Hasashe Na Ina Ganin Yakamata Ka Karbi Kaddara Kai Kwankwaso Ka Rungumi Abokin Ka Kuma Dan Uwanka Domin Ciyar Da Alummar Arewacin Nigeria Gaba, Ina So In Tuna Maka Cewa Bautar Da Dan Ado Yayi Maka Da Sunan Siyasa Sam Bai Cancanci Irin Bakin Halin Da Kake Nuna Masa Ba Kawai Saboda Lokacin Zamansa Wani A Kasar Nan Yayi, Zan Kara Maimaitawa Kayi Hakuri Ka Rungumi Kaddara Ka Koyawa Zuciyar Ka Son Ganin Cigaban Wanin Ka Ko Ba Komai Ka Tsira Da Imanin Ka Domin Hassada Tana Da Alaka Da Shirka In Baa Tuba Ba.
Ina Kira Ga Masu Ruwa Da Tsaki Na Jihar Kano Da Su Yi Zama Na Gaggawa Domin Jawa Yayansu Kunne Musamman Dr Rabiu Musa Kwankwaso Dangane Da Manufarsa Na Son Ganin Bayan Kujerar House Speaker Cewa Wannan Asara Ce Da Ba Iya Kano Ce Zatayi Ba Face AREWA Ta Wani Bangaren Ma Mu Na Iya Cewa Nigeria Bakidaya Saboda Jajurcewar Dan Ado, Wannan Abinda Yakeyi Sam Ba Zai Haifar Masa Da Da Mai Ido Ba Domin Kuwa Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai Yayi.
Kai Kuma Mai Jumurin Zuwa Kotu Kar Ka Fasa, Amma Ka Sani Ba Za Mu Taba Lamunce Mu Ku Ba Dangane Da Al'amuran Ku Na Son Zuciya Domin Ganin Kun Mayar Da Yankin Mu Baya Ba. A Karshe Mu Na Addu'a Allah Ya Ganar Da Mai Hassada
✍️
Gali isah bahawa sopisti