Ibrahim Ahmad abubakar

Ibrahim Ahmad abubakar 799788

11/10/2020

SUNAYEN ALLAH WANDA YAFI SON A
ROKE SHI DASU:
Idan mutum yanason rokon Allah, akwai sunanda
Allah Yafiso ace bawa ya kiraye Shi dashi, wannan
suna shine;
RABBI ko RABBANA.
Wanda duk ya duba cikin Qur'ani Mai Girma zai ga
yadda Annabawa da sauran Salihan bayi s**ayita
rokon Allah da wannan suna, kadan daga ciki sune;
Lokacinda Annabi Adam A.S shida matarsa s**a
saba dokar Allah ta hanasu cin wata itaciya a
Aljannah, da s**a bukaci Gafarar Allah sai s**ace;
ﻗﺎﻻ ﺭﺑﻨﺎ ﻇﻠﻤﻨﺎ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ .
Kuma Allah Ya amsa musu.
Lokacinda Annabi Nuhu A.S yayita wa'azi na tsawon
shekara 950 mutanen sa basuyi Imani ba, sai ya roki
Allah da wannan sunan akan Allah Ya shafesu a
doron kasa. Kuma Allah Ya amsa masa.
ﻭﻗﺎﻝ ﻧﻮﺡ ﺭﺏ ﻻﺗﺪﺭ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺭﺽ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻔﺮﻳﻦ ﺩﻳﺎﺭﺍ .
Annabi Ibrahim A.S da wannan suna yayi amfani
wajen rokon Allah Ya sanya garin Makka ya zamto
mai aminci da yalwan abinci, kuma Allah Ya amsa
masa; shima sai yace;
ﻭﺇﺫ ﻗﺎﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺭﺏ ﭐﺟﻌﻞ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺒﻠﺪ ﺀﺍﻣﻨﺎ .
Annabi Ibrahim A.S da dansa Annabi Isma'il A.S
lokacinda s**a fara gina dakin Ka'aba da wannan
suna s**ayi amfani wajen rokon Allah Ya amsa
musu, kuma Allah Ya tada Manzo cikin garin, kuma
Allah Ya amsa musu, sai s**ace;
ﻭﺇﺫ ﻳﺮﻓﻊ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻭ ﺇﺳﻤﻌﻴﻞ ﺭﺑﻨﺎ ﺗﻘﺒﻞ
ﻣﻨﺎ .
Annabi Zakariyya A.S da zai roko Allah Ya bashi da,
bayan yakai wajen shekara 120 matarsa takai wajen
80-100, ta wuce lokacin haihuwa, sai yayi amfani da
wannan sunan wajen rokon Allah Ya bashi da, kuma
Allah Ya amsa masa, sai yace;
ﻭﺯﻛﺮﻳﺎ ﺇﺫ ﻧﺎﺩ ﺭﺑﻪ ﺭﺏ ﻻ ﺗﺬﺭﻧﻰ ﻓﺮﺩﺍ ﻭﺃﻧﺖ ﺧﻴﺮﺍﻟﻮﺭﺛﻴﻦ .
Annabi Isa A.S da wannan suna yayi amfani wajen
rokon Allah alokacinda mutanen sa s**a bukaci ya
roka musu Allah idan da gaske shi Annabi ne, Allah
Ya sauko musu da tsirre na abinci, kuma Allah Ya
amsa masa;
ﻗﺎﻝ ﻋﻴﺴﻰ ﭐﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺑﻨﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻣﺎﺀﺩﺓﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ .
Annabi Musa A.S da sunan yayi amfani wajen rokon
Allah Ya halaka su Fir'auna da dukiyar su, kuma Allah
Ya amsa masa;
ﺭﺑﻨﺎ ﭐﻃﻤﺲ ﻋﻠﻰ ﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ ﻭﭐﺷﺪﺩ ﻋﻠﻰ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ .
Annabi Yusuf A.S da sunan yayi amfani wajen rokon
Allah Ya sa a kaishi prison akan ya zauna gidan uwar
dakinshi suna neman sa da zina, kuma Allah Ya
amsa masa;
ﻗﺎﻝ ﺭﺏ ﺍﻟﺴﺠﻦ ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻰ ﻣﻤﺎ ﻳﺪﻋﻮﻧﻨﻰ ﺇﻟﻴﻪ .
Annabi Sulaiman A.S da sunan yayi amfani wajen
rokon Allah Ya bashi mulkinda ba za'a sake mai irin
wannan mulkin ba, kuma Allah Ya amsa masa;
ﻗﺎﻝ ﺭﺏ ﭐﻏﻔﺮﻟﻰ ﻭﻫﺐ ﻟﻰ ﻣﻠﻜﺎ ﻻﻳﻨﺒﻐﻰ ﻟﻺﺣﺪﻣﻦ ﺑﻌﺪﻯ .
Annabi Ayyuba A.S da sunan yayi amfani wajen rokon
Allah a lokacinda tsananin ciwo ya kamashi, kuma
Allah Ya amsa masa ya bashi lafiya;
ﻭﺃﻳﻮﺏ ﺇﺫ ﻧﺎﺩﻯ ﺭﺑﻪ ﺃﻧﻰ ﻣﺴﻨﻰ ﺍﻟﻀﺮ ﻭﺃﻧﺖ ﺃﺭﺣﻢ ﺍﻟﺮﺍﺣﻤﻴﻦ .
Annabi Muhammad S.A.W shima da wannan sunan
yayi amfani wajen rokon Allah a lokacinda kafuran
Makka s**a fitine shi, kuma Allah Ya amsa masa;
ﺭﺏ ﻓﻼ ﺗﺠﻌﻠﻨﻰ ﻓﻰ ﺍﻟﻘﻮﻡ ﺍﻟﻈﻠﻤﻴﻦ .
--------------- -------------
Matar Fir'auna da wannan sunan tayi amfani wajen
rokon Allah Ya gina mata gida a Aljanna Ya kuma
kareta daga Fir'auna, kuma Allah Ya amsa mata;
ﻭﺿﺮﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺜﻼ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺀﺍﻣﻨﻮﭐ ﭐﻣﺮﺃﺕ ﻓﺮﻋﻮﻥ ﺇﺫ ﻗﺎﻟﺖ ﺭﺏ
ﭐﺑﻦ ﻟﻰ ﻋﻨﺪﻙ ﺑﻴﺘﺎ ﻓﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ .
Nana Bilkisu mai mulki a zamanin Annabi Sulaiman
A.S itama da wannan sunan tayi amfani wajen
ambaton Allah a lokacin da ta Musulunta.... ﻗﺎﻟﺖ ﺭﺏ ﺇﻧﻰ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻰ ﻭﺃﺳﻠﻤﺖ ﻣﻊ ﺳﻠﻴﻤﻦ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ
ﺍﻟﻌﻠﻤﻴﻦ.
Mala'iku suma da wannan sunan suke amfani wajen
rokawa kansu Imani da gafara;........ ﺭﺑﻨﺎ ﻭﺳﻌﺖ ﻛﻞ ﺷﻰﺀﺭﺣﻤﺔ ﻭﻋﻠﻤﺎ ﻓﺎﻏﻐﺮ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺗﺎﺑﻮﭐ
ﻭﭐﺗﺒﻌﻮ ﺳﺒﻴﻠﻚ ﻭﻗﻬﻢ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﺠﺤﻴﻢ .
Masu Imani ma Allah Ya tabbatar musu cewar da
wannan suna suke rokon Sa, kuma Yana amsa
musu, masu Imani ma s**ace;.......... ﺭﺑﻨﺎ ﻓﭑﻏﻔﺮﻟﻨﺎﺫﻧﻮﺑﻨﺎ ﻭﻛﻐﺮﻋﻨﺎ ﺳﻲﺀﺍﺗﻨﺎ ﻭ ﺗﻮﻓﻨﺎ ﻣﻊ
ﺍﻷﺑﺮﺍﺭ .
Mutanen Annabi Dawud A.S suma sunanda s**ayi
amfani dashi kenan kuma Allah Ya amsa musu Ya
basu nasara akan mutanen Jaluta;
ﻭﻟﻤﺎﺑﺮﺯﻭﭐ ﻟﺠﺎﻟﻮﺕ ﻭﺟﻨﻮﺩﻩ ﻗﺎﻟﻮﭐ ﺭﺑﻨﺂ ﺃﻓﺮﻍ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺻﺒﺮﺍ .
Matasan As habul Kahfi suma da sunanda s**ayi amfani
dashi kenan kuma Allah Ya amsa musu Ya karesu
daga sharrin mutanen su dana azzalumin sarkin su;
ﺇﺫ ﺃﻭﻯ ﺍﻟﻔﺘﻴﺔ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻜﻬﻒ ﻓﻘﺎﻟﻮﭐ ﺭﺑﻨﺎ ﺀﺍﺗﻨﺎ ﻣﻦ ﻟﺪﻧﻚ ﺭﺣﻤﺔ ﻭ
ﻫﻴﻰﺀ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﺭﺷﺪﺍ .
Hatta yan wuta sunanda suke amfani dashi kenan
wajen rokon a saukake musu azaba, amma su Allah
baYa amsa musu saboda sun riga sun zamo yan
wuta;
ﻗﺎﻟﻮﭐ ﺭﺑﻨﺎ ﻣﻦ ﻗﺪﻡ ﻟﻨﺎ ﻫﺬﺍ ﻓﺰﺩﻩ ﻋﺬﺍﺑﺎ ﺿﻌﻔﺎ ﻓﻰ ﺍﻟﻨﺎﺭ .
Shaidan kansa da sunan da yayi amfani kenan wajen
rokon Allah Ya bashi tsawon rai a duniya har ranarda
za'a busa kaho don ya halakarda yayan Annabi Adam
A.S, kuma Allah Ya amsa masa;
ﻗﺎﻝ ﺭﺏ ﻓﺄﻧﻈﺮﻧﻰ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﻳﺒﻌﺜﻮﻥ .
--------------- -------------
Ya Rabbana Ka sanya kasarmu Nigeria hannun
Adalan Shugabanni, Ka bamu zaman lafiya a
kasarmu da garuruwan mu, ka kame hannun
azzalumai Ka mayar musu da kaidinsu a kansu.
Tunatarwa zuwaga wanda basuyi like wannan page kuyi like yanzu dan Allah kuyi share sabida wasu su amfana
allah yasa mudace

23/08/2020

Good morning my friend god bless you

Address

Kano

Telephone

+2348079978802

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim Ahmad abubakar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share