Muhammad Abdullahi Manu DKD

Muhammad Abdullahi  Manu DKD Muhammad Abdullahi Manu

30/06/2022

MULKIN DAI YA KARE!

Arewa babu wutar Mambila!.

Babu ruwan Baro!.

Babu kamfanin Ajaokuta!

Babu Rijiyoyin man Fetur a Bauchi da Gombe!

Babu makarantar Petroleum Training Institute ta Kaduna!

Babu wutar Zungeru!

Babu wutar Mambilla

Babu layin dogon Kano-Kaduna!

Babu layin dodon Kano-Katsina-Maradin jamhuriyar Niger

Babu na Lagos-Maiduguri!

An kasa gyaran Refineries!

An kasa gina sabbin Refineries duk da alkawarin da s**a yi!

An kasa gyara sha'anin ilimi!

Kusan shekara babu karatu a jami'oin mu!

An kasa gyara sha'anin lafiya da Asibitocin Gwamnati!

A yau 12.5kg silindar gas yana farashin Naira N8000+ Gas (diesel) #790 liter!

Shan man fetur a farashin Gwamnati ya zama tashin hankali sai yadda ka samu!

An bada bashin noma amma 'yan ta'adda sun hana noman!

Duk inda shanu suke anbi an sace!

Mun koma sai mun biya 'yan ta'adda haraji kamun su barmu mu zauna a garuruwanmu!

Mun koma sai mun biya 'yan ta'adda haraji kafin su barmu muyi noma!

A Arewa kowa a tsorace yake!

Sun mayar da 'yan Arewa 'yan gudun hijira a cikin Kasar su na asali saboda tsoron Kidnappers!

Sun mayar da hanyar Abuja zuwa Kaduna tarkon mutuwa!

Sun mayar da dazukan Birnin Gwarin jihar Kaduna jamhuriyar 'yan ta'adda!

A yau baka san a tsakanin kai ko iyalinka wa za'a fara kamawa a kashe ba!.

A wani yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas mata sun koma aure da karfi da yaji babu sadaki babu waliyyi!

Arewa ta tashi a tutan babu, 'yan ta'adda duk sun kwace garuruwa da dazuzzuka!

Sunki gyara kamfanonin Arewa, sun ki dakile matsalar hauhawan farashi, sai kokarin rufe boda da hana shigowa da tufafin gwanjo da shinkafa!

Maigaskiya ya zabo mutanen mu, ya basu dukkan dama da karfin iko amma sun gagara, sunci amanar Maigaskiya sunci amanar 'yan Arewa!

Kuma wai a hakan suke so su yaudaremu, su mika mu hannun su Kaka mai karkarwa wadanda zasu mana mulkin kabilanci!

Wannan wani irin mulki ne?
Allah wadaran naka ya lalace!

Amma kuyi hakuri, wani bawan Allah ne ya rubuta ba Datti Assalafiy ba!

Daga Shafin Datti Assalafiy

21/06/2022

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammad Abdullahi Manu DKD posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share